‘Yan Majalisa Za Su Sa Kafar Wando Daya da Gbajabiamila, Ya 'Cinye' 76% a Rabon N7bn
- Akwai yiwuwar Femi Gbajabiamila ya samu sabani da abokan aikinsa a dalilin rabon wasu kudi
- Ana zargin ‘yan majalisa sun samu $15m bayan sun amince a canza salon bashin da ake bin Gwamnati
- Rt. Hon. Gbajabiamila ya samu $11m a cikin Dalolin, sai kowane ‘Dan majalisa sun tsira da $10, 000
Abuja - Wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya sun shirya yin ta ta kare da shugabansu, Femi Gbajabiamila bisa zargin rashin adalci wajen rabon $15m.
Rahoton da aka samu daga Leadership ya tabbatar da cewa an samu sabani a game da yadda za a raba wadannan makudan kudi da aka samu daga gwamnati.
‘Yan majalisar da abin ya fusata, sun fito su na zargin Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da hannu wajen amincewa da canza salon bashin da CBN yake bin Najeriya.
Kamar yadda ‘yan majalisar tarayyar su ka nuna, Gbajabiamila ya amince a rikida bashin N22.72tr da gwamnatin Najeriya ta karba, a karshe ya tashi da $15m.
Rikicin ya jawo shugaban majalisar wakilan ya daga zaman ranar Talata domin ya samu isasshen lokacin da zai iya lallabar wadanda suke tada jijiyar wuyansu.
Kuskuren ranar komawa aiki
Idan rahoton gaskiya ne, Gbajabiamila ya yi ikirarin kuskure wajen sanar da ranar dawowa.
Ana haka sai ga Akawun majalisar tarayya, Yahaya Danzaria ya fitar da jawabi a ya ce ba za ayi zama a lokacin da aka sanar da farko ba, ya ce kuskure aka yi.
Daya daga cikin ‘yan majalisar da suka zanta da jaridar, ya ce mafi yawan ‘ya ‘yan jam’iyyun adawa a majalisar kasar sun shirya yin fito na fito da shugaban.
Zargin da ake yi shi ne bayan ya samu ‘yan majalisa sun amince da rokon da gwamnatin Muhammadu Buhari ta gabatar, an ba Gbaja Dalolin miliyoyi.
An yi rabon kura a Majalisa
Da karbar wannan kudi da ya kusa kai Naira biliyan bakwai, sai aka ce shugaban majalisar ya amince a ba kowane ‘dan majalisar tarayya fam $10, 000.
A karshe abin da ‘yan majalisar suka tashi da shi bai wuce $3.6m, shugaban ya soke sama da $11m shi kadai, a nan ne wasu ke ganin ba ayi adalci a kason ba.
An tuntubi Hadimin shugaban majalisar, Lanre Lasisi, amma bai amsa kiran waya da sakonni ba. ‘Yan majalisa irin Benjamin Mzondu sun ce ba su batun ba.
Takarar Tajuddeen Abbas
A jiya aka ji labari Abubakar Nalaraba ya ce ‘yan majalisa ba su goyon bayan Tajuddeen Abbas ya zama shugaban majalisar domin bai da karbuwa.
Hon. Nalaraba ya ce ‘Dan takaran da APC ta ke so ba sananne ba ne a majalisar wakilai, sannan bai da alaka mai kyau da sauran abokan aikinsa a kasar.
Asali: Legit.ng