Ban Mallaki Gida Ko Guda Ɗaya Ba a Kasashen Ketare, Shugaba Buhari

Ban Mallaki Gida Ko Guda Ɗaya Ba a Kasashen Ketare, Shugaba Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen tunanin ko yana da wasu gidaje a kasashen ketare
  • Yayin da ya karbi bakuncin jakadan Burtaniya a fadarsa, Buhari ya ce bai mallaki gida ko guda ɗaya ba a wajen Najeriya
  • Buhari ya ƙara da cewa Sarki Charles III ya taba tambayarsa idan yana da gida a Ingila amma ya faɗa masa ba bu

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce bai mallaki gida ko guda ɗaya ba a ƙasashen ƙetare har kawo yanzu da yake dab da sauka kan karagar mulki, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Buhari ya yi wannan furuci ne yayin da yake karban takardun amincewa daga Jakadan Burtaniya a Najeriya, Richard Hugh Montgomery da takwaransa na Sri Lanka, Velupillai Kananathan, a Aso Rock ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Dan Daudu Bobrisky Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ya Son Ƙulla Wata Alaƙa Da Abokai

Shugaba Buhari da jakadan Burtaniya.
Ban Mallaki Gida Ko Guda Ɗaya Ba a Kasashen Ketare, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shugaban ƙasa ya bayyana cewa ya taɓa faɗawa sabon sarkin Ingila, Sarki Charles III cewa bai da gida ko ɗaya a kasashen waje a wani lokacin da suka gana da juna.

Buhari ya ce yayin ganawa da Sarki Charles III ya jefo masa tambayar ko yana da gida a nan Burtaniya, ya faɗa masa gaskiya cewa ba shi da ko guda ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa, Shugaba Buhari ya ce:

"A ɗaya daga cikin zaman da na samu yi da Sarki Charles III ya yi mun wata tambaya da ta bani sha'awa cewa ko ina da gida a Ingila, na faɗa masa bani da gida ko guda ɗaya."
"Ba gida kaɗai ba, bani da ko da kwatankwacin inci ɗaya a wata ƙasa daban da Najeriya."

Shugaba Buhari ya ce musayar al'adu da ake samu tsakanin Najeriya da Burtaniya ya samo asali ne tun shekaru masu yawa da suka shuɗe.

Kara karanta wannan

An Fara Musayar Yawu Tsakanin Gwamnatin Buhari da Gwamnan APC Kan Satar Kuɗin Talakawa

Ya ce shi kansa ya amfana da irin haka, inda ya tuna lokacin da ya halarci ɗaukar horon sojoji a makarantar Mons Officer Cadet da ke Aldershot a ƙasar Ingila tsakanin 1962 zuwa 1963.

NNPP Ba ta da Kudin Kalubalantar Nasarar Tinubu a Ƙotu, Buba Galadima

A wani labarin kuma Jigon NNPP ya ce rashin isassun kuɗi ne ya hana jam'iyyar kai ƙara kan zaben shugaban ƙasa 2023

Buba Galadima, ya ce idan kana son kalubalantar nasarar zabe a gaban ƙuliya kana bukatar akalla biliyan N5bn, kuma jam'iyyar NNPP ba ta da waɗan nan kuɗin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262