'Yan Sanda Sun Cafke Mutum Biyu Kan Harin Da Aka Kai Kan Jami'an Amurka a Jihar Anambra

'Yan Sanda Sun Cafke Mutum Biyu Kan Harin Da Aka Kai Kan Jami'an Amurka a Jihar Anambra

  • Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta sanar da cewa ta kama wasu da ake zargin da hannun su kan kisan jami'an ofishin jakadancin Amurka
  • A mummunan harin da aka kai kan jami'an an halaka mutum uku daga cikinsu sai jami'an ƴan sanda mutum huɗu
  • Tawaga ta musamman ta jami'an tsaro aka tura domin farautar miyagun inda suka ƙona sansanin waɗanda ake zargin

Jihar Anambra - Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta bayyana cewa ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi da hannun su kan harin da aka kai kan kwamban motocin ofishin jakadancin Amurka, a ƙaramar hukumar Ogbaru ta jihar.

Binciken farko-farko da ƴan sanda suka gudanar ya tabbatar da an halaka mutum bakwai a harin.

Daga cikin mutum bakwai ɗin, uku jami'an ofishin jakadancin ne sannan huɗu jami'an ƴan sanda ne masu yi mu su rakiya.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma Da Dama a Wani Mummunan Hari a Jihar Kaduna

Yan sanda sun cafke mutum biyu kan kisan jami'an Amurka
Kwamishinan 'yan sandan jihar Anambra, Echeng Echeng Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

Da ya ke magana dangane da lamarin ranar Alhamis, kwamishinan ƴan sandan jihar Anambra, Echeng Echeng, ya bayyana cewa an tura tawagar jami'an tsaro ta musamman zuwa maɓogar waɗanda ake zargin, rahoton Channels Tv ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tawagar ta haɗa da ƴan sanda na musamman, dakarun sojojin ruwa da na ƙasa, inda suka farmaki maɓoyar waɗanda ake zargin a ƙauyen Ugwuaneocha, cikin ƙaramar hukumar Ogbaru

A cewarsa jami'an tsaro na zuwa sansanin sai suka tarar babu kowa a ciki. Sai dai, yayin da jami'an su ke ƙona sansanin, sun cafke wasu mutum biyu waɗanda ke hannun ƴan sanda domin amsa tambayoyi.

Dalilin zuwan jami'an ofishin jakadancin yankin

Kwamishinan ƴan sandan ya kuma bayyana cewa, mutanen da harin ga ritsa da su, mutum biyar jami'an ofishin jakandancin Amurka da jami'an ƴan sanda huɗu daga Legas, suna kan aikin duba illar zaizayar ƙasa ne a Ogbaru, cewar rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tashin Hankali Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Halaka Jami'an 'Yan Sanda a Jihar Imo, Rundunar Ta Dau Mataki

Suna cikin motoci kwamba biyu ne lokacin da mummunan harin ya auku.

Gwamnatin Amurka Ta Yi Martani

A wani rahoton na daban kuma, gwamnatin Amurka ta yi martani kan mummunan harin da aka kai kan jami'anta a jihar Anambra.

Gwamnatin tace harin bai ritsa da ɗan ƙasarta ko ɗaya ba, inda tace tana duba yiwuwar matakin ɗauka na gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng