Kungiyar MURIC Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Kirista Dan Kudu a Shugabancin Majalisar Dattawa

Kungiyar MURIC Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Kirista Dan Kudu a Shugabancin Majalisar Dattawa

  • Kungiyar ‘MURIC’ ta bukaci masu neman takarar shugabancin majalisa su janyewa Kirista daga Kudu
  • Babban Daraktan kungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya sanar da haka a ranar Laraba 17 ga watan Mayu
  • Ya ce a matsayinsu na kungiya mai fada aji, suna kira da a raba mukamai tsakanin addinan biyu

Abuja - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) ta bukaci dukkan Musulmai masu neman takarar shugabancin majalisar dattawa ta 10 da su janyewa dan uwansu Kirista dan Kudu.

Kungiyar ta ce tana goyon bayan bai wa Kirista dan Kudu mukamin shugaban majalisar dattawa ta 10, don samun daidaito a kasar baki daya.

Ishaq/MURIC
MURIC Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Kirista Dan Kudu a Shugabancin Majalisar. hOTO: Daily Post
Asali: Facebook

Babban Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola shi ya fidar da wannan sanarwa a ranar Laraba 17 ga watan Mayu, jaridar Daily Trust ta tattaro.

Daraktan ya yi magana akan tikitin Muslim-Muslim

Kara karanta wannan

Lokacin Mu Ne: Matasan Kiristocin Arewa Sun Fada Wa Tinubu Wanda Suke So Ya Nada Mukamin SGF

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A matsayin mu na kungiya mai fada aji a harkokin kasar nan, mun duba sosai yadda yanayin kasar Najeriya take ganin yadda aka samu cece-kuce akan tikitin Muslim-Muslim da kuma yadda ta kaya.
“Duba da haka, musamman yadda kasar Najeriya take da addinai daban-daban, muna martaba kasarmu akan komai kuma muna goyon bayan a tura shugabancin majalisar zuwa ga Kirista daga Kudu."

A hada kai tsakanin Kirista da Musulmi, inji MURIC

Ya kara da cewa:

“Najeriya na bukatar hadin kai tsakanin Musulmai da Kirista saboda wannan hadin kai din ne kadai zai kawo zaman lafiya da ci gaba a kasar.”

Daraktan ya kara da cewa a matsayinsu na kungiya, basu yarda Musulmai su dauki dukkan mukamai ba a kasar, duk da Musulmai ne suke da rinjaye a kasar amma dole su raba mukamai a tsakaninsu da ‘yan uwansu Kiristoci, jaridar Daily Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Babban Jigon APC Ya Faɗi Ɗan Takarar da Ba Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ba, Ya Faɗi Dalilai

Majalisa ta 10: Gwamna Ganduje Ya Fadi Wanda Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawar Najeriya

A wani labarin, Gwaman jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi karin haske akan wanda zai kasance shugaban majalisar dattawa ta 10 da ake ta cece-kuce akanta, musamman yadda 'yan siyasa ke faman kawo farmaki ga kujerar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar 4 ga watan Mayu inda yace tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma tsohon ministan Neja Delta, Godswill Akpabio ne ake sa ran zai zama shugaban majalisar ta 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.