'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 30 a Wani Sabon Hari a Jihar Plateau
- Ƴan bindiga sun sake kai wani mummunan hari a jihar Plateau, inda suka salwantar da rayukan mutane da dama
- Miyagun ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Tanknale, inda suka halaka mutum 30 da basu ji ba basu gani ba
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce suna ƙoƙarin cafko maharan
Jihar Plateau - Ƴan bindiga sun halaka sama da mutum 30 a ƙauyen Tanknale, cikin ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.
Jaridar Daily Trust ta yi rahoto cewa, kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Talata.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Alabo ya bayyana cewa kwamishinan ƴan sandan jihar, Bartholomew Onyeka, ya bayar da umurnin tura jami'an tsaro zuwa yankin.
Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Budewa Jami'an Ofishin Jakadancin Amurka Wuta a Anambra, Sun Halaka Mutane Da Dama
Kakakin ya bayyana cewa sun samu labarin harin ne ta hannun wani jami'in ɗan sanda a ƙauyen na Tanknale, cewa ƴan bindigan suna ta harbe-harbe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda harin ya faru
A kalamansa:
"Ranar Talata da misalin ƙarfe 11:56 na dare, mun samu kiran gaggawa daga ɗaya daga cikin jami'an mu da ke a ƙauyen Tanknale, cikin ƙaramar hukumar Mangu, cewa ƴan bindiga sun bude wuta a wani ƙauye dake makwabtaka da su."
"Nan da nan kwamishinan ƴan sanda ya tura da jami'an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da cewa an cafke masu hannu a harin domin su fuskanci fushin hukuma.
Jami'an tsaro sun fatattaki ƴan bindigan
Lokacin da mataimakin kwamishinan ƴan sandan jihar mai kula da binciken manyan laifuka, ACP Bawa Sale, ya ziyarci ƙauyen, ya ce ƴan bindigan sun ranta a na kare inda suka bar mota guda ɗaya da babura guda huɗu, cewar rahoton Aminiya.
Kwamishinan ƴan sandan jihar ya kuma buƙaci mutanen yankin da su kwantar da hankulansu, inda ya ƙara da cewa suna duk mai yiwuwa domin ganin sun cafko miyagun ƴan bindigan.
Ya kuma buƙace su da duk mai wani bayani mai muhimmanci ya ba wa jami'an tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace.
'Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Ofishin Jakadancin Amurka
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki kan jami'an ofishin jakadancin Amurka na Najeriya, a jihar Anambra.
Ƴan bindigan sun halaka mutum huɗu a yayin harin, sannan suka yi awon gaba da wasu daban kuma.
Asali: Legit.ng