Najeriya Ta Samar Da Magungunan Yaƙi Da Cutar Sikila Da Hawan Jini
- Ma'aikatar kimiyya da fasaha ta ƙasa ta sanar da samar da magungunan cutar sikila da kuma na hawan jini
- Ministan ma’aikatar Olorunnimbe Mamora ne ya sanar da haka a lokacin da yake gabatar da jawabi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
- Ana sa ran magungunan za su taimaka wajen rage yawaitar samun masu fama da cutar sikila da ta hawan jini a Najeriya
Abuja - Ministan Kimiyya da Fasaha, Olorunnimbe Mamora, ya ce ma’aikatarsa ta samar da hanyoyin ganowa da kuma magance cututtukan sikila da hawan jini.
Ciwon sikila cuta ce ta jini da ke shafar 'haemoglobin' wato sinadaran cikin jini da ke rarraba iskar 'oxygen' zuwa sassa daban-daban na jikin ɗan adam.
Mun samo hanyar da za a bunƙasa noman abinci
Mamora ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 17 ga watan Mayu, a fadar shugaban ƙasa, yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron da fadar shugaban ƙasar ta shirya, kamar yadda ICIR Nigeria ta wallafa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ministan ya kuma ce ma’aikatarsa ta samu gagarumar nasara a ɓangaren sarrafa kayan abinci da kuma samar da hanyoyin da za a bunƙasa harkar noman abincin, PM News ta ruwaito.
A cewarsa:
“Najeriya ƙasa ce mai yawan jama’an da ke fama da cutar sikila da kuma masu ɗauke da cutar, a bisa hakan ne muka samar da maganin cutar daga tsirai da za su iya hana cutar tasiri domin rage yawan ciwukan da cutar ke haifarwa.”
Mun samu hanyar binciko cutar ta sikila
A cewarsa:
“Ta amfani da ɗakunan gwaje-gwajenmu na zamani, mun samar da hanyoyin gano cutar saboda matakin farko na kula da majinyaci, shi ne gano cutar da ke damunsa.
"Idan ba ka gano abinda ke damun mutum ba, ba zaka iya masa maganin abin da ba ka sani ba.”
Najeriya na cikin kasashe mafi yawan cutar sikila
An ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ke a kan gaba wajen masu fama da cutar sikila a duniya.
Kimanin mutane miliyan 50 ne ke ɗauke da cutar sikila a duniya. Najeriya na da mutane kusan miliyan huɗu zuwa shida da ke fama da cutar.
A kowace shekara, ana haihuwar yara kusan 300,000 da suka kamu da cutar sikila a duk duniya. Ƙasashen kudu da hamadar sahara na kan gaba da kusan kashi 75% cikin 100% na adadin.
Gwamnatin tarayya za ta cefanar da asibitin fadar shugaban ƙasa
A wani labarin da muka wallafa a baya, wasu rahotanni na nuni da cewar gwamnatin tarayya ta yi yunƙurin siyar da asibitin fadar shugaban ƙasa.
Hakan dai na da alaƙa da fafutukar da gwamnatin ta ke yi na neman hanyoyin samun ƙarin kuɗaɗen shiga.
Asali: Legit.ng