'Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Ofishin Jakadancin Amurka Na Najeriya a Jihar Anambra

'Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Ofishin Jakadancin Amurka Na Najeriya a Jihar Anambra

  • Ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki kan jami'an ofishin jakandancin Amurka na Najeriya a jihar Anambra
  • Ƴan bindigan sun halaka jami'an ofishin mutum biyu sannan suka halaka ƴan sandan da ke tare da su mutum biyu
  • Miyagun ƴan bindigan sun kuma sace jami'an ƴan sanda mutum biyu da kuma direban ɗaya daga cikin motocin jami'an

Jihar Anambra - An bindige wasu daga cikin ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka na Najeriya, a ƙaramar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra.

Majiyoyi sun tabbatarwa da jaridar Daily Trust cewa an buɗewa tawagar motocin ma'aikatan wuta ne, lokacin da suke wucewa ta yankin.

'Yan bindiga sun halaka jami'an ofishin jakadancin Amurka a jihar Anambra
Miyagun 'yan bindigan sun halaka mutum huɗu a harin Hoto: Guardian.com
Asali: UGC

Wani majiya ya bayyana cewa suna kan aikin jinƙai ne a yankin, yayin da wata majiyar tace jami'an suna ƙoƙarin zuwa inda za su je ne yayin da suke wucewa ta Ogbaru.

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari a Abuja, Sun Sace Mutane Da Dama

"Aƙalla mutum huɗu ne suka halaka a harin, yayin da wasu da dama suka samu raunika. Jami'an tsaro sun yi wa yankin ƙawanya." A cewar wata majiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa lamarin ya auku ne ranar, Talata a ƙaramar hukumar Ogbaru ta jihar.

Ikenga ya bayyana cewa Ƴan bindiga sun bindige jami'an ofishin jakadancin na Amurka mutum biyu, da ke aikin jinƙai a yankin. Sannan sun halaka jami'an ƴan sandan Police Mobile Force (PMF), mutum biyu, cewar rahoton The Guardian.

Ya kuma ƙara da cewa ƴan bindigan sun cinnawa gawarwakin mutanen wuta, tare da motocin su, inda ya ce suna hango jami'an tsaro, sai suka sace jami'an ƴan sanda biyu da direban ɗayar motar, suka ranta ana kare.

Kara karanta wannan

Rai Ya Yi Halinsa Yayin Da Fada Ta Barke a Tsakanin Jami'an EFCC a Sokoto

Ofishin jakandancin na Amurka, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa jami'ansa na ba jami'an tsaro haɗin kan da ya dace domin shawo kan matsalar.

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Abuja, Sun Sace Mutane Da Dama

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun sake kai hari a birnin tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da mutane da yawa.

Ƴan bindigan a lokaci harin da suka kai cikin tsakar dare ƙauyen Pegi na ƙaramar hukumar Kuje, sun sace mutum 15.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng