Jami'in EFCC Ya Gamu Da Ajalinsa Wajen Fada Da Abokan Aikinsa a Sokoto

Jami'in EFCC Ya Gamu Da Ajalinsa Wajen Fada Da Abokan Aikinsa a Sokoto

  • Wani jami'in hukumar EFCC ya ce ga garin ku nan bayan faɗa ya ɓarke tsakaninsa da wasu abokan aikinsa
  • Jami'an dai sun ba hammata iska ne kan ajiyar wasu kaya na wani wanda ake zargi da ya ke a tsare
  • Tuni hukumar ta dakatar da sauran jami'an yayin da aka tura su gaban kotu domin fuskantar hukunci

Jihar Sokoto - Wani jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), sufeto Abel Isah Dickson, ya gamu da ajalinsa bayan faɗa ya ɓarke tsakaninsa da wasu abokan aikinsa su biyu.

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa faɗan ya ɓarke ne kan ajiyar wasu kaya da suka haɗa da maganunguna da tsabar kuɗi.

Jami'in EFCC ya rasa ransa wajen fada da abokan aikinsa a Sokoto
Jami'an hukumar EFCC Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Tuni dai aka maka sauran jami'an biyu, Apata Oluwaseun Odunayo da Ogbuji Titu Tochukwu, a gaban wata kotu a jihar Sokoto kan laifin kisan kai, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Sabuwar Rigima Ta Ɓalle a Jam'iyyar APC Kan Zaben Shugaban Kasa, Bayanai Sun Fito

Shugaban hukumar EFCC na ƙasa, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa ba zai yi ƙasa a guiwa ba, har sai ya tabbatar da an hukunta jami'an.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin yayin ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, ya ce an dakatar da jami'an da aka yi faɗan da su.

Yadda jami'in ya gamu da ajalinsa

Uwujaren ya ce jami'in ya rasu ne a ranar 7 ga watan Mayun 2023, a asibitin koyarwa na jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto inda ake duba lafiyarsa saboda raunikan da ya samu.

Kakakin ya ce mamacin ya samu raunikan ne kwanaki biyu kafin rasuwarsa a faɗan da ya ɓarke, tsakaninsa da abokan aikinsa, Apata Oluwaseun Odunayo da Ogbuji Titu Tochukwu.

Ya ce sun samu saɓani ne kan ajiyar kayan wani wanda ake zargi da ya ke a tsare, wanda har ya kai su ga ba hammata iska.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini

Gobara Ta Tashi A Ofishin Hukumar EFCC

A wani labarin na daban kuma, gobara ta kama a ofishin reshen hukumar EFCC na jihar Enugu.

Gobarar ta kama ne dai a dalilin tashi da saukar wutar lantarki, inda ta lahanta ɗaya daga cikin gine-ginen da ke a ofishin hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng