Ana Fargabar da Yawa Sun Mutu a Wani Kazamin Harin Yan Bindiga a Jihar Filato
- Yan bindiga sun kai kazamin hari kauyen Kubat a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato sa'ilin da mutane ke bacci
- Gwamna Simon Lalong ya yi Alla-wadai da sabon harin kana ya umarci hukumomin tsaro sun kamo yan ta'addan
- Ya kuma umarci hukumomin jin kai su ziyarci kauyen da lamarin ya faru domin gano abinda ya dace gwamnati ta agaza musu da shi
Plateau - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai mummunan hari ƙauyen Kubat da ke yankin ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato, Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana fargabar mutanen kauyen da yawa, wanda ya kunshi mata da ƙananan yara sun rasa rayukansu sakamakon harin.
Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan sun kai farmaki ƙauyen a daidai lokacin da mutane ke bacci da daddare.
Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini
Gwamna Lalong ya fusata, Ya ɗauki matakai
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ayyana sabon harin da 'yan bindiga suka kai da babban abin takaici da nadama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lalong, mamban jam'iyyar APC mai mulki, ya umarci hukumomin tsaro su farauci maharan kuma su tabbata sun damƙe su baki ɗaya.
A wata sanarwa da darektan yaɗa labarai na ofishin gwamna, Dakta Makut Simon, ya fitar, Lalong ya ɗauki matakin agazawa mutanen da harin ya shafa.
Gwamnan ya umarci hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA) da hukumar samar da zaman lafiya su ziyarci yankin da harin ya shafa su tattara bayanan taimakon da talakawa ke buƙata.
A cewarsa, ta hanyar binciken abinda ya faru da asarar da jama'a suka yi ne kaɗai gwamnati zata samu damar rage wa mutane raɗaɗin kuncin rayuwar da suka shiga.
Har yanzun jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Filato, DSP Alabo Alfred, bai ce komai ba kan adadin yawan mutanen da suka rasa rayuwarsu a harin.
Yan Bindiga Sun Saba Saiti, Sun Bindige Abokin Aikinsu a Kano
A wani rahoton da muka kawo muku, kun ji cewa yan bindiga sun yi yunkurin sace wani bawan Allah da ɗansa a jihar Kano
Rahoton yan sanda ya nuna cewa maharan sun yi yunkurin harbe ɗan amma sai harsashin ya sauka kan abokin aikinsu, ya mutu nan take.
Asali: Legit.ng