Yan Bindiga Sun Saba Saiti, Sun Bindige Abokin Aikinsu a Kano

Yan Bindiga Sun Saba Saiti, Sun Bindige Abokin Aikinsu a Kano

  • Wasu yan bindiga sun kai hari gidan wani magidanci a kauyen Yarimawa, ƙaramar hukumar Tofa a jihar Kano
  • Yayin da suka yi yunkurin sace mutumin da ɗansa, suka harbi abokin aikinsu har lahira bisa kuskure
  • Kwamishinan yan sanda ya ce jami'ai sun kama waɗanda ake zargi kuma sun amsa laifukansu

Kano - Jami'an yan sanda sun cafke wasu 'yan bindiga uku bisa zargin yunkurin sace Mahaifi da ɗansa a kauyen Yarimawa, karamar hukumar Tofa a jihar Kano.

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne bayan 'yan bindiga sun kutsa kai gidan wani bawan Allah, Nasiru Yahaya, suka yi kokarin garkuwa da shi da ɗansa, Gaddafi Nasiru.

Bajen Yan sanda.
Yan Bindiga Sun Saba Saiti, Sun Bindiga Abokin Aikinsu a Kano Hoto: Policeng
Asali: Twitter

Yayin haka ne Gaddafi ya musu tirjiya, wanda hakan ya haddasa faɗa a takaninsu. A kokarin harbe ɗan, maharan suka bindige ɗaya daga cikinsu bisa kuskure, nan take ya faɗi matacce.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kan Mutane a Arewa, Gwamnan APC Ya Fusata Ya Ɗau Mataki

Yadda lamarin ya faru a kauyen Yarimawa

Da yake nuna waɗanda ake zargin, kwamishinan rundunar yan sanda reshen jihar Kano, (CP), Muhammed Usaini Gumel, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun samu labarin 'yan bindiga sun shiga gidan Nasiru Yahaya a kauyen Yarimawa, karamar hukumar Tofa a Kano, suka yi kokarin sace shi da ɗansa, Gaddafi Nasiru."
"Ana haka ne ɗan ya musu tirjiya, da suka yi nufin harbe shi, sai kawai suka bindige abokin aikinsu mai suna, Umar Abdullahi Ɗanbaba, nan take ya sheƙa barzahu."
"Ganin haka magidancin ya tsere, sun harbi mutum biyu a ƙafa yayin da suka kawo ɗauki. An kai waɗanda suka jikkata Asibiti domin kulawa da lafiyarsu."

Yadda yan sanda suka damƙe yan bindigan

CP ya kara da cewa:

"Yayin bincike, dakaru suka kama waɗan nan mutanen; Idris Abdullahi (26) daga Janguza a Tofa LG, Tukur Yusuf (40) daga ƙauyen Langyal a yankin Tofa, da kuma Ilyasu Aminu ɗan kauyen Gargai a karamar hukumar Bebeji."

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini

Sun bayyana abinda ya ja suka kai harin

Da suke bayanin amsa laifinsu, 'yan bindigan sun ce wani ɗan garin ya kira su, ya nemi su je gidan su sace magidanci da ɗansa.

Ɗaya daga cikinsu ya ce:

"Mun je gidan kamar yadda aka umarce mu amma ɗan ya ƙi yarda, mun so harbe shi amma sai muka harbe ɗan uwanmu. Ban taba shiga irin wannan aikin ba, wannan ne na farko kuma na yi nadama."

A wani labarin kuma mun kawo muku rahoton cewa Kotu Ta Garkame Fitaccen Malamin Musulunci a Gidan Gyaran Hali a Bauchi

Wata Kotun majirtire ta umarci a tsare Sheikh Idris Dutsen Tanshi a kurkuku har zuwa lokacin zama na gaba kan karar da aka shigar ana zarginsa da kalaman ɓatanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262