Kotu Ta Garkame Fitaccen Malamin Musulunci a Gidan Gyaran Hali a Bauchi
- Wata Kotun Majistire a jihar Bauchi ta umarci a tsare Sheikh Idris Abdul'aziz a gidan gyaran hali gabanin zama na gaba
- Rundunar yan sandan jihar ne suka gurfanar da shi a gaban Ƙuliya kan zargin kalaman ɓatanci ga fiyayyen halinta
- Wannan na zuwa ne wata ɗaya bayan ɗage zaman tattaunawa tsakanin Shiekh Idris da sauran malamai
Bauchi - Kotu ta tsare fitaccen Malamin addinin Musulunci na Bauchi kuma babban limamin Masallacin Jumu'a Dutsen Tanshi, Dakta Idris Abdulaziz, a gidan gyaran hali.
Daily Trust ta rahoto cewa an tsare Malamin a gidan Yari ne bisa zargin yana amfani da wasu kalamai a karatuttukansa da ka iya tunzura jama'a.
Da yake tabbatar da haka, Lauyan Malamin, Barista Umar Hassan, ya ce rundunar yan sandan Bauchi ce ta gurfanar da Dakta Idris a gaban Kotun Majistire ranar Litinin.
Barista Hassan ya ce Alkalin Kotun ya ƙi aminta da bukatar Beli, inda ya umarci a tafi da Malamin zuwa gidan gyaran hali kuma gobe idan Allah ya kaimu Talaka a dawo da shi gaban Kotu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
BBC Hausa ta rahoto cewa Ɗakta Idris ya amsa gayyatar rundunar 'yan sanda kafin daga bisani su gurfanar da shi a gaban Kotu.
A wani wa'azi da ya yi a cikin watan Ramadan, Sheikh Idris ya faɗi wasu kalamai da suka haddasa cece kuce da muhawara mai zafi tsakanin mabiya addinin Musulunci.
Wasu daga cikin Malaman Musulunci sun fassara Kalaman Sheikh Idris da miyagun kalaman batanci ga fiyayyen halinta, Annabi Muhammad (SAW).
Wasu Malami sun buƙaci mahukunta su gaggauta kama shi kan waɗannan kalamai da ya yi yayin da wani sashin malaman kuma suka goya masa baya.
Idan baku manta ba, a wancan lokacin hukumar kula da harkokin shari'ar Musulunci a Bauchi ta shirya zaman titsiye Malamin amma daga baya ta ɗaga saboda wasu dalilai.
A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya ta kafa sharuddai ganain kwaso ragowar yan ƙasa daa rikicin da ya ɓarke a ƙasar Sudan.
Gwamnatin tarayya ta zo da sabon tsari kan jigilar ɗauko yan Najeriya daga Sudan. FG ta kafa sabbin muhimman sharuɗda wanda wajibi kowa ya cika gabanin jirgi ya kwaso saura.
Asali: Legit.ng