Mutane 38 Sun Rasa Rayukansu a Jihar Nasarawa a Wani Rikicin Manoma Da Makiyaya
- Mutane 38, ciki har da wani Fasto aka kashe a wani hari da aka kai wasu ƙauyuka biyu a jihar Nasarawa
- An ce harin ya samo asali ne sakamakon rikici tsakanin wani manomi da wani makiyayi, wanda ya yi sanadin mutuwar makiyayin
- Gwamnatin jihar ta yi Allah-wadai da kashe-kashen, ta kuma sha alwashin hukunta waɗanda suka aikata laifin
Nasarawa - Wasu 'yan bindiga da suka kai hari a daren Alhamis, a kauyukan Talakafia da Gwanja da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, sun kashe mutane 38, ciki har da shugaban wata majami’a da kuma mata da ƙananan yara.
Harin wanda aka fara tun ƙarfe 9 na dare har zuwa safiyar Juma'a, ya samo asali ne sakamakon rashin jituwa da aka samu tsakanin wani manomi da makiyayi.
Makiyayin ya kora shanunsa cikin gonar manomin
Leadership ta wallafa cewa makiyayin ne ya kora shanunsa don yin kiwo cikin a gonar gyaɗa da masarar manomin, manomin ya yi masa magana, amma sai makiyayin ya ciro wuƙa da nufin ya sari manomin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hakan ya fusata manomin, inda daga nan ne faɗa ta kaure a tsakaninsu, wanda a cikin haka manomin ya yi nasarar ƙwace wuƙar daga hannun makiyayin gami da halaka shi da ita.
A wani mataki na ramuwar gayya da ‘yan uwa da abokanan makiyayin suka ƙaddamar, sun far wa mazauna kauyukan, inda suka kashe mutane 38 tare da jikkata wasu da dama. Waɗanda harin ya rutsa dasu sun haɗa da mata da kananan yara.
Za a hukunta waɗanda suka kai harin
Mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Emmanuel Akabe, ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa inda lamarin ya faru a ranar Asabar domin jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa.
Ya yi Allah wadai da harin tare da shan alwashin cewa za a gurfanar da waɗanda suka kai harin gaban kuliya.
Harin dai shi ne na baya bayan nan a rikice-rikice da kan ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya.
Meye tushen rikicin?
Rikicin na da nasaba da faɗaɗa wuraren kiwo ga shanu daga makiyaya, wanda hakan kan janyo asarar rayuka da dama, rahoton Punch.
Ya kuma raba dubban mutane da muhallansu. An yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin magance musabbabin rikicin da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Rikicin makiyaya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 8 a Borno
A wani labarin mu na baya, aƙalla mutane takwas ne aka bayyana mutuwarsu gami da kuma kona gidaje 47 a wani rikicin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Bayo ta jihar Borno.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ne ya bayyana hakan a wani taro da shuganannin ƙungiyar Miyetti Allah da ta manoma suka shirya a Maiduguri.
Asali: Legit.ng