Da Dumi-Dumi: 'Yar Najeriya Ta Kafa Tarihin Lokaci Mafi Tsawo Da Aka Kwashe Ana Dafa Abinci
- Kwararriyar mai dafa abinci ƴar Najeriya, Hilda Baci, ta kankaro wa Najeriya daraja a idon duniya, yayin da ta karya tarihin lokaci mafi tsawo da aka kwashe ana dafa abinci
- A yayin da haziƙar ƴar Najeriyar ta wuce tarihin wanda aka taɓa kafawa a baya na sa'o'i 87, mintuna 45 da daƙiƙa 00, mutanen da ke wajen sun cika da shewa
- Sai dai, Hilda ta cigaba da girkinta domin ba tarihin da aka kafa a baya tazara mai nisa, yayin da agogon ya cigaba da ƙirga lokacin da ta kwashe a gaban mutane
Shahararriyar mai dafa abinci ƴar Najeriya, Hilda Baci, ta karya tarihin lokaci mafi tsawo da aka kwashe ana girki wanda Lata Tondon, mai dafa abinci ƴar ƙasar India ta kafa na sa'o'i 87, mintuna 45 da daƙika 00.
Shiri Ya Kwabe: Magidanci Ya Yi Wa Babbar Kawar Matarsa Juna Biyu, Ta Sha Alwashin Sai Ta Haiho Jaririn
Abin ban sha'awa shine har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, ba ta dakata ba, ta cigaba da yin girkin, inda yanzu har ta samu sa'o'i 87, mintuna 50 da daƙiƙa 37, kuma ba ta tsaya ba.
A yayin da ta ke cigaba da girkinta, akwai ƴan Najeriyan da suka taru a wajen domin ƙara ƙarfafa mata guiwa.
Bidiyon yadda girkin na ta ke gudana, ya nuna mutane na ta shewa domin nuna tsantar farin cikin su kan jajircewar da ta nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hilda ta zama sananniya
A tsawon kwana huɗu da suka gabata, girkin da ta ke yi ya haɗa ƴan Najeriya daga ɓangarori da dama, waɗanda suka taru a wajen domin ganin yadda ta ke girkin na ta.
Mutanen da suka kwana a wajen da ta ke girkin sun cigaba da tafa mata, inda suka gargaɗe ta da ta bi a sannu tun da ta karya tarihin.
A kowane lokaci dai Hilda za ta iya dakatawa tun da ta samu nasarar karya tarihin.
Bahaushen Kano ya kafa tarihi, ya zama makaho na farko da ya zama farfesa a Najeriya
A baya mun kawo mu ku rahoto, kan yadda wani Bahaushe daga jihar Kano ya kafa wani sabon tarihi a Najeriya.
Farfesa Jibrin Isah Diso, ya zama makaho na farko a tarihin Najeriya da ya kai matsayin farfesa.
Asali: Legit.ng