Duniya Juyi-Juyi: Mutumin da Ya Fara Mallakar Biliyoyin Daloli a Afrika Ya Sauka, Ya Koma Can Kasan Dangote

Duniya Juyi-Juyi: Mutumin da Ya Fara Mallakar Biliyoyin Daloli a Afrika Ya Sauka, Ya Koma Can Kasan Dangote

  • Patrice Motsepe, dan Afrika na farko da ya fara mallakar biliyoyin daloli yanzu shi ne na 1,284 a jerin attajirai na Forbes
  • A baya, ya kasance na 1,153 bayan Dangote, dan Arewa kuma attajirin da ya fi kowa kudi a duniya kana na 131 a duniya a yanzu
  • Motsepe dan kasar Afrika ta Kudu ne, kuma kudinsa na zuwa daga fannin hako, wasanni da dai dauran harkalloli

Patrice Motsepe ya sauka zuwa matsayi na 1,284 a jerin attajiran duniya na Forbes da ke bin diddigin attajiran duniya.

Motsepe ya kafa tarihin kasancewa attajirin farko bakar fata dan Afrika da ya fara mallakar biliyoyin daloli a 2008 har ya shiga jerin attajirai na Forbes yana da shekaru 46.

A cewar rahoton Forbes na ranar Lahadi 14 ga watan Mayu, Motsepe yana da kudin da yanzu sun kai $2.4bn, inda ya samu raguwar dukiya da $800m daga abin da ya mallaka na $3.2bn a 2023.

Kara karanta wannan

Arziki Nufin Allah: Jerin Kamfanoni 10 Mallakin Dangote da Ko da Wasa Baku Sani Ba

Yadda attajiri farko a Afrika ya tsiyace
Yadda dukiyarsa ke hawa da sauka | Hoto: @forbes
Asali: Facebook

Idan aka kwatanta da Aliko Dangote, a yanzu Dangoye na da zunzurutun kudi har $13.6bn.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wanene Patrice Motsepe?

Patrice Motsepe, attajiri ne mai kudi a bangaren hakon ma’adinai. Shi ne mu’assasin kamfanin African Rainbow Minerals da kuma African Rainbow Capital da ke harkar zuba hannun jari.

Motsepe na kuma da hannun jari a kamfanin Sanlam da ke harkar kudade, kuma shine shugaba kana mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Mamelodi Sundowns.

A 2021, Motsepe ya zama zababben shugaban kungiyar gamayyar kwallon kafa ta Confederation of African Football.

Meye ya faru da dukiyarsa?

Rahotanni sun bayyana cewa, dukiyarsa ta ragu ne sakamakon disashewar karfin harkallarsa ta ARM da ke rike da 39.7% na dukiyarsa.

ARM wani katafaren kamfanin hakon ma’adinai ne da ke Afrika ta Kududa ta dukufa wajen hako karfe, gawayin kwal, karafan kofa, gwal, da sauran duwatsu masu daraja.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Roki Majalisa Ta Bada Damar Ya Karbo Aron $800m a Karshen Mulkinsa

Bincike ya bayyana cewa, hannun jarin ARM ya sauka da 20% tun farkon shekarar nan, inda ya sauka daga R288 ($14.92) a ranar 1 ga watan Janairu zuwa R230.56 ($11.94) ya zuwa yau.

Dangote na da wasu kamfanoni 10 na daban

A wani labarin, kunji yadda rahoto ya yi tsokaci ga wasu manyan kamfanoni mallakin Dangote da ba kowa ne ya san su ba.

An ruwaito cewa, wasu kamfanonin ya saye su ne baya ga uwar kamfanin da ya mallaka na Dangote Group.

Rahoton da muka hada ya ba da jerin kamfanonin guda 10, kamar yadda rahotanni suka kawo a makon nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.