Kaico: Matashi Ya Aika Mahaifiyarsa Kiyama Saboda Sabanin da Suka Samu a Kan ₦10,000

Kaico: Matashi Ya Aika Mahaifiyarsa Kiyama Saboda Sabanin da Suka Samu a Kan ₦10,000

  • Wani matashi ya hallaka mahaifiyarsa bayan samun sabani a kan kudin da bai taka kara ya karya ba
  • Bayanansa sun nuna bai ma yi dana-sanin aikata bakin aikin ba, ya ce a shirye yake ya mutu saboda haka
  • Ba wannan ne karon farko da ake samun mummunan yanayi irin wannan ba, ya sha faruwa a lokuta da dama

Jihar Ribas - Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta kwamushe wani matashi mai suna Osaro Owate, bisa zarginsa da kasan mahaifiyarsa a unguwar Alesa da ke karamar hukumar Eleme a jihar, biyo bayan takaddama kan kudi ₦10,000.

Wanda ake zargin, ya yi ikirarin cewa yana fama da matsalar hauka ta aljanu sama da shekaru 30, ya kuma amsa cewa ya yi amfani da fartanya ne wajen kashe mahaifiyar tasa, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

"Ka yi hauka ne?": Tashin hankali yayin da mawaki ya kaftawa dan sandan Najeriya mari

Da yake magana a gajeren faifan bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, Owate ya ce ya bukaci mahaifiyar tasa ce ta ba shi ₦20,000, domin sayen kayan sawa don halartar wani bikin biso, sai ta bashi ₦10,000.

Yadda matashi ya sheke uwarsa a Ribas
'Yan sandan Najeriya a bakin aiki | Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

Bayanai daga bakin matashin

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A jiya (Jumma’a) na gaya mata cewa da safiyar yau (Asabar) ta je ta ciro kudin ta bani zan siya kayan sawa don bikin bsio. Washe gari da sassafe kafin na farka ta bar gidan ta ce za ta yi wurin bison.
“Kuma na tambaye ta game da kudin da na nema ko ta fasa bani ne ba ta son na halarci bison. Tace to zata ciro kudin ta bani.
“Ta je ta ciro ₦20,000 da na je na same ta, ta ba ni ₦10,000 kacal. Na fara tunanin inda zan je naga tufafin ₦10,000 na saya.”

Kara karanta wannan

"Da Na Kowa Ne": Uwa Ta Fadi Yadda Lakcara Ya Kore Ta a Aji Don Kukan Jinjiranta, Bidiyon Ya Janyo Cece-Kuce

Mahaifiyar ta zage shi

Hakazalika, matashin ya koka da yadda mahaifiyar tasa ta zage shi saboda bai da takamaiman sana’ar da yake yi don kula da kansa.

Ya kara da cewa:

“Sadda nake bin ta, sai ta fara zage-zage na cewa abokaina suna aiki amma me ya sa har yanzu ba ni da aikin yi. Na tunatar da ita cewa ina da matsala ta da ke damuna. Ta yaya zan je neman aiki alhali ina da matsalar da ta dame ni?
“Ta ci gaba da surutu sai na fusata na buge ta da fartanya. Tana cikin madafa tana girka abinci ne na buge ta.
“Da fushi ya harzuka ni na karasa ta. Idan rayuwata za ta kare saboda wannan, ta kare kawai. Ina fama da matsalar aljanu sama da shekaru 30. Kamar yadda kuke gani yanzu, ina so in mutu.”

'Yan sanda basu bayyana komai ba

Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ba ta fitar da wata sanarwa ba kan wannan mumunan lamarin har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A baya ban taba samun wani matashin da ya hallaka mahaifiyarsa, amma ya gamu da fushin alkali bayan da aka gurfanar dashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.