Sojoji Sun Gano Wani Makeken Rami Da Yan ISWAP Suka Birne Makamai Masu Dimbin Yawa A Sambisa
- Rundunar sojin hadin guiwa ta ‘Operation Hadin Kai’ ta gano tarun makamai a karkashin kasa da aka boye
- Majiyoyi daga rundunar ce suka tabbatar da haka inda suka ce an samu muggan makamai masu yawa
- An tabbatar da cewa da yawa daga maboyan ‘yan ta’addan an lalata su musamman wadanda suka hada da Garno da Farisu
Jihar Borno - Rundunar sojin hadin guiwa ta ‘Operation Hadin Kai’ ta tabbatar da gano wasu tarun makamai a karkashin kasa daga kungiyar ISWAP a cikin dajin Sambisa da ke jihar Borno.
A cikin rahoton Zagazola Makama da ke buga bayanai dangane da nasarorin rundunar ta bayyana cewa rundunar sojin sun bankado tarun makaman ne a karkashin kasa bayan kai samame a zangon Ukuba da ke yankin karamar hukumar Bama a ranar Asabar 13 ga watan Mayu.
Majiyoyi daga rundunar ta ce an samu muggan makamai da suka hada da bama-bamai da makamai masu kado jirgin sama da guruneti guda 50 da sauran makamai masu hatsari a ramin da aka boye su.
Sauran makaman sun hada da kayayyakin hada bama-bamai da kuma harsasai akalla 183 duk a cikin ramin, cewar jaridar TheCable.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sojojin sun kashe dan ta'adda daya
Daya daga cikin ‘yan ta’addan ya mutu yayin da aka kwace bindigarsa AK-47 da sauran kayayyaki dake da alaka da makamai daga gare shi.
Majiyar ta rundunar sojin ta ce jam’an sojin da suke aiki a yankin Sambisa zuwa Timbuktu da kuma yankin Tabkin Chadi sun samun nasarar mamayar yankin ta kasa yayin da kuma suke samun agaji daga jiragen sama wanda hakan ya kara ba su daman matsawa ‘yan ta’addan.
Da yawa daga maboyan ‘yan ta’addan an lalata su musamman wadanda suka hada da Garno da Garin Doctor da Farisu da kuma Somalia.
Sauran sun hada da Ukuba da Garin Glucose da Garin Ba’aba da Njumia Izzah da kuma Bula Abu Amir.
Sojoji Sun Sheke Shugaban 'Yan Bindiga, Da Kwamushe Masu Ba Su Bayanan Sirri
A wani labarin, Rundunar Sojin hadin gwiwar sama da kuma ta kasa sun kai wani farmaki cikin daji inda suka hallaka shugaban 'yan bindiga a yankin.
Rundunar ta kuma sheke 'yan bindiga 14 tare da kwamushe shugaban nasu a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Asali: Legit.ng