Ma'aikatan Jihar Zamfara Sun Gudanar Da Salloli Na Musamman Kan Rashin Biyan Albashi
- Tura ta kai bango ga ma'aikatan jihar Zamfara, inda suka koka kan yadda aka riƙe mu su albashin su ba a biya ba
- Ma'aikatan sun shirya Salloli na musamman domin neman taimakon Allah ubangiji su samu a ba su haƙƙoƙinsu
- Ma'aikatan sun koka kan halin ƙuncin da suka tsinci kan su, inda suka ce rabon su da albashi tun watan Janairu
Jihar Zamfara - Wasu ma'aikatan gwamnatin jihar Zamfara sun gudanar da Salloli na musamman, a masallacin idin Gusau, babban birnin jihar ranar Asabar.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ma'aikatan sun taru a masallacin idin ne da misalin ƙarfe 10 na safe, inda suka nemi Allah ya kawo mu su ɗauki kan kuɗaɗen albashinsu.
Ma'aikatan sun bayyana cewa, rabon da a ba su albashi tun watan Janairu, wanda hakan ya jefa su cikin halin ƙaƙanikayi.
Wani daga cikin ma'aikatan wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa da kyar su ke iya samun abun sanyawa a bakin salati, cewar rahoton Tribune.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce wannan Sallar da suka yi, sun yi ta ne domin neman taimako wajen Allah, ya sanya gwamnan jihar da duk wasu masu ruwa da tsaki, da su tausaya mu su, su ba su ƴan haƙƙoƙinsu.
A kalamansa:
"Da yawan mu mun kusa fara bara, ba mu iya samun abinda za mu ci ko sau ɗaya a rana. Wannan Sallar ta musamman ta mu ka gudanar, mun yi ta ne domin neman Allah ya sanya gwamnan mu, ƴan majalisar dokoki da duk wasu masu hannu a ciki, da su ji tausayin mu."
"Mun sha wuya sosai a dalilin wannan ƙangin da mu ka tsinci kan mu, wasu da da yawa sun rasa rayukan su, ba mu son hakan ya cigaba da faruwa. Mun taru a nan ne ba tare da la'akari da bambancin addini ba domin neman Allah ubangiji ya kawo mana ɗauki."
Ƙoƙarin jin ta bakin gwamnatin jihar, kafin kammala haɗa wannan rahoton ya ci tura, domin layin wayar kwamishinan watsa labarai na jihar, Ibrahim Dosara, a rufe ya ke.
Jerin Gwamnoni Masu Barin Gado Da Za Su Bar Magadansu Da Biyan Bashin Albashin Ma'aikata
A wani rahoton na daban kuma, mun jeranto gwamnoni masu barin gado da za su bar magadansu da kwantan biyan bashin albashin ma'aikata.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, na ɗaya daga cikin gwamnonin da ma'aikatan jihar su, ke bin su bashin albashi.
Asali: Legit.ng