“Ka Kunce Ne, Ka Yi Hauka Ne?”: Bidiyo Ya Yadu Na Yadda Mawaki Ya Kaftawa Dan Sandan Najeriya Mari

“Ka Kunce Ne, Ka Yi Hauka Ne?”: Bidiyo Ya Yadu Na Yadda Mawaki Ya Kaftawa Dan Sandan Najeriya Mari

  • Wani bidiyo ya nuna lokacin da mawakin Legas ya kaftawa dan sandan Najeriya mari a bainar jama’a a cikin jihar ta Legas
  • ‘Yan sanda sun ce ba za su jure wannan cin mutuncin ba, dole za su dauki matakin da ya dace don gaba
  • Ba wannan ne karon farko da ake cin zarafin jami’in tsaro da ke bakin aiki ba a Najeriya, hakan ya sha faruwa

Jihar Legas - Wani bidiyo ya yadu a kafar sada zumunta na yadda mawaki Seun Kuti ya kaftawa dan sandan Najeriya mari a jihar Legas.

Seun, wanda da ne ga fitaccen mawakin Fela ya fusata, inda aka ga yana fuskantar dan sanda tare ture shi da kirji har ta kai ya mare shi.

A wani sashe na bidiyon, dan sandan duk da hakurinsa da yadda ya yi shuru, mawakin ya kafta masa mari.

Kara karanta wannan

Ya Ci Kamu: Fasto Ya Jawo Cece-Kuce Bayan Bayyana Kiyayyarsa Ga Bola Tinubu

An umarci a kamo Kuti saboda marin dan sanda
IGP ya ce a kamo masa Kuti bayan da ya mari dan sanda | Hoto: @PoliceNG and David Corio/Redferns
Asali: UGC

An ji yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Baka da hankali ne? Ka yi hauka ne?”

Kamar yadda yake a bidiyon, dan sandan bai rama ba, inda ya tsaya ya kama kuncinsa yana kallon ikon Allah.

Duba da abin da ya faru, alamu sun nuna ‘yan sanda sun tsayar da Kuti ne shingen binciken ababen hawa da suka saba a tituna.

Girman laifin da ya aikata daga bakin lauya

A bangare guda, wani lauyan kare hakkin bil-adama, Festus Ogun ya siffanta abin da ya faru da cin zarafin jami’in tsaro da ke bakin aiki kuma hakan ya saba doka.

Ga abin da lauyan ya shaidawa wakilin Legit.ng:

“Wannan ba daidai bane. Cin zarafi ne kuma ya kamata a yi Allah-wadai da hakan da kakkausar murya. Ban damu da yanayin ba, babu wani dalili na cin zarfi da cutar da jami’in dan sanda da bai tada hankali ko nuna damuwa a fuskarsa ba.

Kara karanta wannan

Mata Ta Sumar Da Mijinta Bayan Ta Lakada Masa Duka a Jihar Lagos

“Wannan lamari ne na cin zarafi balo-balo a dokance. Wannan laifin babba ne saboda ya faru ne da jami’in doka da ke bakin aiki.”

‘Yan sanda sun magantu

A lokacin da Legit.ng ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, CSP Olumuyiwa Adejobi ya ce bai samu labarin bidiyon ba tukuna.

Daga baya, ya fitar da wata sanarwar da ke tabbatar da hakan tare da cewa, sufetan ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba ya umarci a kwamushe Seun Kuti nan take.

Hakazalika, ya ce ‘yan sanda ba za su jure wannan cin mutuncin ba, dole za a dauki mataki mai tsaurin gaske game da hakan.

Ba wannan ne karon farko ba, akwai wani lokacin da wani mai mota ya banke dan sanda ya yi tafiyarsa ba tare da tsayawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.