“Najeriya Ba Ta Kai Inda Ake Tsammaninta Ba Tun Bayan Samun ’Yancin Kai”, Inji Obasanjo
- Tsohon shugaban kasar Najeriya na tunanin cewa, ya kamata ‘yan Najeriya su yi rayuwa yadda ya kamata ake kallon kasar a matsayin uwa a Afrika
- Baban Iyabo, kamar yadda ake kiransa ya ce ‘yan Najeriya a zamaninsa sun iya yanke shawari mai kyau wajen zaban shugananni
- Ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi hadin kai, wanda yace shi ne kadai maganin duk wata matsala a kasar nan
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce ‘yan Najeriya a zamaninsa sun yi zaben shugabanni na gari da suka dace sabanin abin da ake gani a yanzu.
Ya bayyana hakan ne a wurin bikin ba da lambar yabo ta National Daily Awards da aka gudanar a yau Juma’a 12 ga watan Mayu a jihar Legas.
Obasanjo ya kuma bayyana cewa, a zamaninsa an ga gogaggun ‘yan siyasa da ke fafutukar samar da shugabannin da suka dace.
Jaridar Vanguard ta ruwaito shi yana cewa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Bal ma, a wurin zabin shugananni, ‘yan Najeriyan bayan samun ‘yancin kai sun zabi shugabannin da suka dace. Duk mun sani cewa idan zabinku ya yi kyau, aiki da sakamakon da za a samu zai yi kyau.”
Ana yiwa Najeriya kyakkyawan zato
Tsohon shugaban ya bayyana cewa, shugabannin duniya na da fata na gari ga Najeriya bayan da ta samu ‘yancin kai. Ya kuma ce, amma Najeriya bata kai inda ake tsammanin za ta je ba tukuna.
Obasanjo ya kara da cewa:
“A lokacin da firayinministan wancan lokacin ya tafi majalisar dinkin duniya bayan samun ‘yancin kai, duniya ta alanta Najeriya a matsayin uwa ga rana, ba ma uwa ga Afrika ba.”
Ya kuma bayyana wasu tambayoyin da ke kira ga ‘yan Najeriya su yi nazari tare da gano inda matsalolin Najeriya da kuma daukar matakan gyara ba tashin hankali ba.
Ci gaba na zuwa a kasar da ake zaune lafiya
A bayaninsa, Obasanjo ya ce, daga abin da ya koya a aikinsa na kwantar da tarzoma da wanzar da zaman lafiya shine, kasar da ke zaune lafiya, cikin aminci ce ke iya ci gaba
Ya kuma bayyana cewa, yana da kyau kowacce kasa ta mai da hankali ga adalci, daidaito da kuma mutunta juna, rahoton Punch.
'Yan Najeriya na daban ne, inji Obasanjo
Daga nan, ya siffanta ‘yan Najeriya da wasu kalan mutane na daban da ke iya cimma komai suka tunkara a duniya.
Sai dai, ya yi kira ga a gyara abu daya da ke damun mutane da yawa, inda yace kowa ya rungumi hadin kai da taimakon kasar ta ci gaba yadda ya kamata.
A zaben bana, Obasanjo ya nuna goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi.
Asali: Legit.ng