Ya Ci Kamu: Fasto Ya Jawo Cece-Kuce Bayan Bayyana Kiyayyarsa Ga Bola Tinubu
- ‘Yan Najeriya sun fara tofin Allah-tsine ga wani bidiyon da ya yadu na fasto Kassy Kachukwu na cocin Peniel da ke sukar Bola Ahmad Tinubu
- Malamin na coci ya ce, da tun farko matar Tinubu, sanata Remi Tinubu ta zuba ma zababben shugaban guba a abinci da yanzu ba a shiga kitimurmura a zaben 2023 ba
- ‘Yan Najeriya suna da kira a kama faston, domin hakan ya saba da aikin Allah da kuma kira ga zaman lafiya
Benin, jihar Edo – ‘Yan Najeriya da yawa sun yi ta martani mai zafi game da bidiyon da ya yadu na fasto Kassy Kachukwu na cocin Peniel da ke birnin Benin a jihar Edo.
An jifaston an cewa, da tun farko matar zababben shugaban kasa, Remi Tinubu ta ba mijinta guba da ba a kai ga rikicin da ake ciki na waye ya lashe zabe ba a gaban kotun zabe.
Ya kara da cewa, idan Allah ya rada wa matan dukkan gurbatattun ‘yan siyasa yadda za su basu guba, da Najeriya ta kasance cikin aminci.
Fasto na son matar Tinubu ta zuba masa guba a abinci
A wani bidiyon da @AderonkeW ta yada a Twitter na faston, ta ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Kassy Chukwu na cocin Peniel da ke birnin Benin, ya tsaya a kan dandamalin cocinsa sannan yace da ya kamata sanata Oluremi Tinubu tun farko ta ba zababben shugaban kasa Bola Tinubu guba!
“’Yan a mutun Obi, wannan shine karshe wajen mugunta. Obi ya dasa kiyayya da yawa a cikin mabiyansa. Ya Allah, ka kare Tinubu, Amin.”
Martanin ‘yan Najeriya
A sashen martani, ‘yan Najeriya da yawa sun bayyana ra’ayinsu game da wannan batu da ke fitowa daga bakin malamin addini.Ga kadan daga ciki:
Graceman Debo Adeleye:
“Akwai bukatar cikin gaggawa a kame tare da bincikar wanna faston.”
John Chadwick Jr. Akainza:
“Na ga wannan bidiyon kuma sai da na kusan faduwa saboda muninsa, wadannan mutanen ba kananan mugaye bane duba da yadda suke magana kan wannan abin duka.
“Babban abin kunya ne kuma abin takaici ga duniyar kiristoci gaba daya.”
AY Dot:
“Kiyayyar a biye take, dama akwai ta, amma a sarkafe. Tafiyar Obidient ta kara bayyanawa da kuma nuna abin a zahirance ne.”
Matthew Adejare:
“Sun dauki mummunan kiyayya yadda ba a tsammani, babu dadin ji.”
A tun farko, wani fasto ya ce Obi ne Allah ya zaba, amma 'yan Najeriya suka tubure suka zabi son ransu.
Asali: Legit.ng