Iyalai Sun Baiwa Hammata Iska Kan Kudin Sadakin Diyarsu N250,000
- Yan uwan juna sun haɗu sun lakaɗa wa ɗan uwansu dukan tsiya kan kuɗin sadaki N250,000 da surukinsu ya biya a Delta
- Mutumin ya bayyana cewa bai san hawa ba bai san sauka ba yan uwansa suka kama jibgarsa da makami
- Hukumar yan sandan jihar Delta ta tabbatar da faruwar lamarin amma har yanzu ba'a kama waɗanda ake zargi ba
Delta - Ana zargin wani kurtun ɗan sanda da 'yan banga sun yi wa ɗan uwansu mai suna, Uchenna Nmakwe, jina-jina kan kuɗi N250,000 a ƙauyen Akwukwu-Igbo, ƙaramar hukumar Oshimili ta arewa, jihar Delta.
City Round ta tattaro cewa waɗanda ake zargin sun naƙasa ɗan uwan nasu ne a wurin taron iyalai kuma suka ƙwace kuɗin sadaƙin ɗiyarsu N250,000, wanda Surukinsu ya biya.
Yadda lamarin ya faru
Yayin da yake labarta yadda lamarin ya faru, Uchenna, ya yi zargin cewa 'yan uwansa sun yi amfani da makamai biyu, adda da guduma, suka lakaɗa masa na jaki kan kuɗin sadakin.
"Mahmud Yakubu Tsohon Yaro Na Ne," Pater Obi Ya Fallasa Maganar da Ya Faɗa Wa Shugaban INEC Gabanin Zaben 2023
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A jawabinsa, Mista Uchenna ya ce:
"Surukin mu ya gaya mana ba ya bukatar mu shirya wani shagalin biki saboda aurensa da aka ɗaura ranar 7 ga watan Mayu, 2023."
"Kuɗin sadakin da suka kawo naira N250,000, sun tura a asusun bankin babban yayanmu shiyasa bamu raba su tun a ranar ba."
Mutumin ya ƙara da cewa har gidan kakansa suka zo suka same shi, suka kama dukansa da waɗannan makamai bai san hawa ba kuma bai san sauka ba.
A rahoton Punch, mutumin ya ci gaba da cewa:
"Ina zaune a gidan kakana da karfe 6:00 na yamma, yan uwana su uku, Anthony Nmakwe, Ezindu Nmakwe, da Chinedu Nmakwe suka kawo mun hari da adda, guduma da bindiga, suka gwaɓe bakin Mahaifina da guduma."
" Antony ne shugaban ƙungiyar 'yan banga a Akwukwu-Igbo; Chinedu kuma yana aikin ɗan sanda, shi kuma Ezeidu ɗan banga ne, har yanzun yan sanda sun ƙi kama su."
Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?
Kakakin yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ƙara da cewa tuni aka kai Kes ɗin hedkwatar 'yan sanda ta jiha.
"Bamu kama waɗanda ake zargi ba, da farko kwamandan yankin ya kama yan uwan mutumin amma rashin kayan rike su shiyasa ya sake su, amma yanzu Kes din na gaban Hedkwata."
An yi garkuwa da shugaban APC
A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki a Jihar Kudu, Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC
Yan bindigan da ba'a san ko su waye ba sun yi garkuwa da shugaban APC na kauyen Umuarugo.a jihar Imo, Honorabul Chinedu Eleliam.
Asali: Legit.ng