An Yi Mamaki Yayin Da Gwamnatin Buhari Ta Ware N22.4bn Don Ciyar Da Fursunoni
- Dakta Shuaib Belgore ya bayyana cewa gwamnati za ta kashe kuɗaɗe a gidajen gyaran halin da ke a sassa daban-daban na ƙasar nan
- Ya kuma ce turo masu ƙananun laifuka na daga cikin dalilan da suke sa a samu cunkuso a gidajen gyaran halin Najeriya
- Shuaib ya kuma ce akwai buƙatar gina sabbin gidajen gyaran hali gami da duba batun bayar da beli
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta kashe N22.4bn wajen ciyar da fursunonin gidajen gyaran halin da ke a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Babban sakatare a ma'aikatar harkokin cikin gida, Dakta Shuaib Belgore ne ya bayyana hakan, a wajen taron kwana biyu kan batun rage cunkuso a gidajen gyaran hali da aka yi ranar Alhamis a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Kamar yadda Channels TV ta wallafa, Belgore ya ce an riga da an saka waɗannan kuɗaɗe a cikin kasafin shekarar 2023.
Akwai cunkoso a wasu gidajen gyaran halin
Ya kuma ƙara da cewa ana samun ƙaruwar cunkoso, wanda akan samu a gidan gyaran halin cewa 80% cikin 100% na fursunoni duk masu jiran shari'a ne.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kamar yadda ya bayyana, ya ce akwai gidajen gyaran hali 224 a ƙasar baki ɗaya, waɗanda kuma suke ɗauke da fursunoni 75,507 wanda hakan ke nuni da cewa akwai cunkoso a 82 daga cikinsu.
Ya kuma ƙara da cewa akwai fursunoni maza 73,821 da kuma fursunoni mata 1,686 a gidajen gyaran halin.
Belgore ya kuma ce, daga cikin fursunoni 75,507 da ake da su, 52,436 na jiran shari'a ne, 23,071 kuma waɗanda aka yankewa hukunci ne, a yayin da ake da 3,322 da aka yankewa hukuncin kisa.
Gidajen gyaran hali na bukatar garambawul
A cikin rahoton da The Nation ta buga, Belgore ya ce akwai buƙatar ayi wasu gyare-gyare a gidajen gyaran halin ƙasar nan, ciki kuwa har da zamanantar da gidajen domin samun damar gyara halayen fursunonin da ke ciki yadda ya kamata.
Ya kuma bayyana cewa turo masu ƙananan laifuka da ake yawan yi na daga cikin abubuwan da ke ƙara haddasa cunkuso a gidajen gyaran halin.
Ya ce tuntuni masu ruwa da tsaki suka nuna buƙatar a gina wasu sabbin gidajen sannan a sake duba tsarin bayar da beli.
An tura matashi zuwa gidan gyaran hali
A wani labarin kuma, wata kotun majistare ta yankewa wani matashi hukuncin zama gidan gyaran hali bisa laifin zagin mahaifinsa.
Kotun ta tura matashin mai kimanin shekaru 35 zuwa gidan gyaran hali bayan amsa laifin da ake tuhumarsa.
Asali: Legit.ng