Gwamna Masari ya nada VC na jami'ar UMYUK da shugaban Kwaleji
- Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya yi manyan naɗe-naɗe biyu a bangaren ilimi kwanaki kaɗan gabanin sauka daga mulki
- Masari ya naɗa sabon VC na jami'ar Umaru Musa Yar'adua (UMYU) da sabon shugaban kwalejin fasaha ta Hassan Usman Katsina
- Ya yi kira ga ma'aikata, ɗalibai, ƙungiyoyi da sauran al'ummar jihar su baiwa sabbin shugabannin haɗin kai
Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Ballo Masari, ya naɗa sabon mataimakin shugaban jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua (UMYU) da shugaban kwalejin fasahar Hassan Usman (HUK) da ke Katsina.
Gwamnan ya naɗa Farfesa Shehu Salihu Muhammad a matsayin sabon VC na jami'ar UMYU Katsina da kuma Aminu Kallah Doro a matsayin shugaban HUK Poly.
Rahoton jaridar Leadership ya ce wannan naɗi na kunshe a wata sanarwa da sashin kula da harkokin ilmin manyan makarantu na jihar Katsina ya fitar ɗauke da sa hannun babban Sakatare, Surajo Abubakar Dalhatu.
Ya ce naɗin shugabannin biyu ya yi daidai da tanadin sashi na 5(2) a kundin dokokin jami'a 2006 da 25 (1) da ke cikin kundin dokokin kwalejin fasaha 2003 wanda aka yi wa garambawul.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan babban Sakataren ya ce naɗin ya biyo bayan tsallake duk wani siraɗi da dokokin da aka kafa makarantun a kansu suka tanada. Za su shafe wa'adi ɗaya na shekaru biyar.
Gabanin naɗa shi VC na jami'ar UMYU, Muhammad ya kai matsayin Farfesa a fannin kimiyyar siyasa a jami'ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato.
A ɗaya bangeren kuma sabon shugaban kwalejin fasaha ta Hassan Usman, Aminu Kallah Doro, ya riƙe kujerar mataimakin shugaba har zuwa yanzun da ya samu karin girma.
Masari ya aike da sako ga ma'aikata, ɗalibai, da ƙungiyoyi
Dalhatu ya ce:
"Gwamna ya yi wa sabbin shugabannin fatan samun nasara a zangon mulkinsu kana ya roki masu gudanarwa, malamai, ɗalibai, ƙungiyoyi da sauran jama'a su haɗa hannu da su wajen kawo ci gaba a makarantun biyu."
An gudanar da taron Addu'o'i
A wani labarin kuma Al'ummar jihar Katsina da shugabannin PDP sun gudanar da taron addu'ar tunawa da Umaru Musa Yar'adua
A ranar Jumu'a 5 ga watan Mayu da ta gabata, tsohon shugaban ƙasan ya cika shekaru 13 da rasuwa.
A cewar waɗanda suka shirya taron, sun yi haka ne domin ƙara tuna alkhairan tsohon shugaba Yar'adua.
Asali: Legit.ng