Gwamnati Ta Dauki Nauyin Maniyyatan Kiristoci 300 Zuwa Isra’ila Da Jordan Don Sauke Farali A Enugu

Gwamnati Ta Dauki Nauyin Maniyyatan Kiristoci 300 Zuwa Isra’ila Da Jordan Don Sauke Farali A Enugu

  • Gwamnatin Enugu ta dauki nauyin akalla maniyyata hajjin Kiristoci 300 don kai ziyara kasashen Isra’ila da Jordan
  • Gwamnan ya bukaci maniyyatan da kada su manta da jiharsu da kuma kasa baki daya a cikin addu’o’insu
  • Magatakardan hukumar ya yi jawabi, inda ya yabawa gwamnan da cewa mutum ne mai son addini da taimako

Jihar Enugu - Gwamnatin jihar Enugu ta dauki nauyin maniyyata aikin hajjin kirista na bana 300 zuwa Isra’ila da Jordan.

Gwamnan jihar, Ifeanyi Ugwuanyi ne ya fadi hakan a lokacin da ya ke zantawa da maniyyatan Kiristoci 300 zuwa kasa mai tsarki ta Isra’ila da kuma Jordan.

enugu
Ifeanyi Ugwuanyi, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Gwamnan ya bukaci maniyyatan da su yi wa jiharsu addu’a da kuma fatan nasara ga gwamnati mai jiran gado ta Dakta Peter Mbah, a cewar Punch da muka samu.

Kara karanta wannan

Yadda Ganduje Ya Tattara Kayan Gwamnati, Yana Saidawa Iyalinsa – Kwamitin Abba

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Allah a cikin ikonsa da rahamarsa, ya kare mana jiharmu da kuma wannan gwamnati na tsawon shekaru da nayi ina jan ragamarta, jihar ta kasance wacce tafi kowace jiha zaman lafiya.”

Gwamnan ya kara da cewa maniyyata 300 sun tafi Isra’ila don su godewa ubangiji bisa soyayyarsa da rahama a tsawon shekaru takwas da suka wuce, inda ya ce a matsayinsa na Kirista na kwarai, gwamnatinsa ta cika alkawuran da ta dauka.

Mun ji dadi, mun gode

A nasa bangaren, Magatakardar Hukumar Alhazan Kiristoci ta Najeriya, Rev. Yakubu Pam ya nuna jin dadinsa game da hubbasa da gwamnatin Ugwuanyi ta yi ta bangaren addini tun daga kafa gwamnatinsa shekaru takwas da suka wuce.

Rahoton da Vanguard ta ruwaito ya kara da cewa hubbasan gwamnan don tabbatar da cewa jiharsa ce ta fara jigilan maniyyata a kowane lokaci, shine musabbabin nasarar da hukumar ke samu a kasar.

Kara karanta wannan

Ku Rungumi Kaddara, Basarake Ya Fadawa Masoyan Obi, Atiku, Su Bi Bayan Tinubu

Magatakardan a karshe ya shawarci maniyyatan da su yi taka-tsan-tsan don kiyaye aikata wasu ayyuka da zasu jawo abun kunya ga jiharsu da ma kasa baki daya.

Kudin Hajjin bana zai kusan Naira miliyan 3

A wani labarin, hukumar aikin hajjin Musulmai ta bayyana adadin kudaden da za a kashe a hajjin bana.

Ta bayyana cewa, ana bukatar kowane mai niyya ya biya N2.99m domin kujerar hajjin wannan shekarar.

Ana yawan sanya kudi mai jawo cece-kuce na hajji a Najeriya, musamman bayan annobar Korona.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.