Yan Sanda Sun Kai Samame Mabuyar Yan Damfara Ta Intanet, Sun Damke 8 Cikinsu

Yan Sanda Sun Kai Samame Mabuyar Yan Damfara Ta Intanet, Sun Damke 8 Cikinsu

  • Rundunar ‘yan sanda a jihar Rivers ta yi nasarar kwamushe wasu bata gari da suka addabi yankunansu
  • Kakakin rundunar ce ta tabbatar da haka yayin da ta ce bayanan sirri da suka samu ne ya basu wannan nasara
  • Ta ce wadanda aka kaman dukkansu basu wuce shekaru 17 zuwa 22 ba, kuma dukkansu maza ne

Jihar Rivers - Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ta tabbatar da kama wasu wadanda ake zargi da damfara ta yanar gizo da garkuwa da mutane a unguwar Cypo cikin karamar hukumar Etche da ke jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko ce ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta fitar a Port Harcourt a ranar Laraba 10 ga watan Mayu.

yan sanda
Yan Sanda, Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Iringe-Koko ta ce an kai samamen ne a ranar Talata 9 ga watan Mayu bayan samun bayanan sirri, wadanda ake zargin basu wuce tsakanin shekaru 17 da 22 ba, rahoton ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Mummunan Karshe: Jami’an ’Yan Sanda Sun Sheke Wasu ’Yan Bindiga Har Lahira a Fitaciyyar Jihar Kudu

Sanarwar da aka fitar

“Munyi amfani da bayanan sirri da muka samu inda muka kai samame a maboyar masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan damfara a unguwar Cypo a kauyen Umuebule da ke karamar hukumar Etche,” in ji Grace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotannin da muka samu sun ce Iringe-Koko ta bayyana sunayen wadanda aka kaman kamar haka, Desmond Williams mai shekaru 19, da Isaac Patrick 22, da Prince Nelson 17, sai John Ahmed 17.

Sauran sun hada da ThankGod Neesogho 22, da Christian Adewale 22, da Uche Alaga 16, sai kuma Nwika Fakae 22, dukkansu maza.

Iringe-Koko ta ce jami’ansu sun kwato wani matashi dan shekara 20 da aka yi garkuwa da shi bayan da suka yaudareshi cewa zasu bashi aikin yi.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Wadanda muka kaman sun bayyana mana yadda suke yi wajen yaudaran mutane su damfare su ta hanyoyi daban daban wadda ya hada da ta kafar yanar gizo da kuma zuwa da mutanen da basu ji ba basu gani ba maboyar don su zama musu garkuwa”

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An sace shugaban karamar hukuma a Arewa, an kashe dan sandan bayansa

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Okon Effiong ya shawarci iyaye da su kula da abokan ‘ya’yansu da sauran al’amuransu don gudun faruwar irin wadannan muggan halaye.

Yan Sanda Sun Sheke Kasurgumin Dan Bindiga a Jihar Kaduna

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta yi nasarar bindige wani kasurgumin dan bindiga tare da raunata wasu.

Bayan nasarar halaka dan bindigan, jami'an kuma sunyi nasarar kwace babur din da suke amfani da shi wurin zirga zirga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.