An Ji Dalilin Jinkirin Kwanaki 7, Buhari Ya Fasa Dawowa Daga Ingila Saboda Ganin Likita

An Ji Dalilin Jinkirin Kwanaki 7, Buhari Ya Fasa Dawowa Daga Ingila Saboda Ganin Likita

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kara shafe wasu kwanaki a Landan saboda uzurin lafiya
  • Femi Adesina ya ce mai gidansa ai tsaya a Birtaniya ne da nufin Likitan hakori zai cigaba da duba shi
  • Da zarar an gama aikin da ake yi masa a asibiti, Mai girma Muhammadu Buhari zai dawo bakin aiki

England - Shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita wa’adin ziyarar da ya kai birnin Landan a dalilin ganin Likita da yake so ya yi.

A rahoton da aka samu daga Daily Trust a ranar Talata, an ji Mai girma shugaban na Najeriya ba zai dawo gida lokacin da aka sa rai ba.

Hadimin shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar da jawabi a jiya, ya sanar da halin da ake ciki.

Buhari
An shiryawa Buhari liyafa a Landan Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Jawabin Femi Adesina

A matsayinsa na mai magana da yawun Muhammadu Buhari, Mista Adesina ya ce ana duba hakoran shugaban kasar a Birtaniya.

"Shugaban Muhammau Buhari zai zauna a Landan a kasar Birtaniya na karin tsawon mako guda a dalilin Likitan hakori da yake duba shi.
Kwararren Likitan ya bukaci ya sake ganin shugaban (Muhammadu Buhari) nan da kwanaki biyar saboda wani aiki da aka soma yi masa.
Buhari ya hadu da sauran shugabannin kasashen Duniya wajen halartar bikin nadin Sarki Charles III a ranar 6 ga watan Mayu 2023.”

- Femi Adesina

Jaridar Vanguard ta kawo gajeren jawabin da aka fitar daga fadar shugaban kasa a yammacin jiya.

Watakila Osinbajo zai jagoranci FEC

Sanarwar ta na nufin Muhammadu Buhari ba zai samu halartar taron majalisar zartarwa watau FEC da ya saba jagoranta a duk Laraba ba.

Watakila sai zuwa mako mai zuwa shugaban zai halarci wannan zama da bayan shi Ministoci za su sauka daga kujerunsu, a jira wata gwamnati.

"Ba na maimaita aji" - El-Rufai

Da ake batun kafa sabuwar gwamnati, an rahoto Nasir El-Rufai ya ce ko an yi masa tayin zama Ministan Abuja, ba zai karbi wannan mukami ba.

A shekarunsa, Malam Nasir El-Rufai ya nuna ya tsufa da ya rika fama da rushe-rushe, sai dai a nemi wani matashi mai jini a jika ko matashiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng