Karfin Hali: Tsohon Dan Dambe Ya Tuna Baya, Ya Mangare Matarsa a Kan 'Remote' Din TV

Karfin Hali: Tsohon Dan Dambe Ya Tuna Baya, Ya Mangare Matarsa a Kan 'Remote' Din TV

  • Moses Olapade ya yi ta naushin matarsa Atinuke a fuska har sai da ya ga ta dena motsi
  • Makwabtan su ne suka ruga cikin gidan domin cetonta daga hannun mijin bayan sanar da su da 'yaransu suka yi
  • 'Yan sandan jihar ta Ondo sun yi nasarar cafke Moses wanda yanzu haka yake hannunsu

Ondo - 'Yan sanda a garin Akure jihar Ondo sun cafke tsohon ɗan dambe Moses Olapade mai shekaru 56 bisa lakaɗawa matarsa duka da ya yi.

Majiyar mu ta ce ɗan damben wanda yanzu yana tuƙa babbar mota ne ya lakaɗawa matarsa Atinuke dukan tsiya bayan dawowa gida daga tafiya da ya yi.

yan sanda
'Yan sandan Najeriya. Hoto: Tribune
Asali: UGC

Olapade ya nemi matar tasa ta bashi remot ɗin talabijin

Daily Trust ta bada rahoton cewa mutumin ya buƙaci matar ta hannanta masa remot ɗin talabijin ɗin su ne a yayin da ita kuma matar mai shekaru 44 ta hana shi.

Kara karanta wannan

“Kai Kuwa Ka More”: Wani Matashi Ya Ɗora Bidiyon Mahaifinsu Na Musu Rabon Gado

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Olapade wanda yakan kai kaya zuwa Arewacin Najeriya ya dawo bayan sati biyu ya hau matar tasa da naushi a fuska saboda fushin da ya yi.

'Ya 'yansu ne suka fita waje da gudu suka kira maƙwabtansu waɗanda da ƙyar suka ƙwaci matar a hannun mijin nata.

Sai da aka kai matar asibiti

Wani daga cikin makwabtan wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa manema labarai cewa afkawa suka yi cikin gidan domin ceto matar.

A faɗar sa:

“Mun sameta kwance a ƙasa bata motsi a lokacin da muka isa cikin gidan, dole muka yi sauri muka kaita asibitin dake kusa da gidan.”

Jaridar Tribune ta ce wani makwabcin da baya so a bayyana sunansa ya shaida mata cewa mijin ne ya biya duka kudaden maganin da aka kashe kafin jami'an tsaro su yi ram da shi.

Kara karanta wannan

"Ni Ba Kowa Bane Idan Ba Ki" Matashi Ya Roki Tsohuwar Budurwarsa Da Sako Mai Sosa Zuciya, Ya Fusata Samari

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar ta Ondo Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce yanzu haka wanda ake zargi yana hannunsu.

An dakatar da hakimin da ya lakaɗawa matarsa duka

A wani labarin mai kama da wannan da muka wallafa can a kwanakin baya, an dakatar da hakimin wani ƙauye da ya lakaɗawa matarsa dukan da yayi sanadiyar ajalinta a jihar Bauchi.

An dai dakatar da hakimin ne biyo bayan 'yan banga da haɗin gwuiwar wasu jami'an tsaron yankin sun kama shi sannan suka miƙa shi hannun 'yan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng