Mutane 8 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Haɗarin Kwale-kwale a Zamfara

Mutane 8 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Haɗarin Kwale-kwale a Zamfara

  • Yara bakwai da mace guda ɗaya ne dai suka rasa rayukansu a haɗarin kwale-kwalen da ya faru a garin Gusau jihar Zamfara
  • Masu ceto sun yi nasarar ceto mutane huɗu da rai, a yayin da suka tsamo takwas da suka riga mu gidan gaskiya
  • Kwamishinan ruwan jahar ta Zamfara Ibrahim Isa, ya musanta batun da ake na cewar akwai matsalar ruwan sha a Gusau

Gusau - Mutane takwas ne dai aka tabbatar da mutuwarsu a wani haɗarin kwale-kwale da ya rutsa da su a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Abba Shehu, wani wanda ya shaida faruwar lamarin ya shaidawa Punch a ranar Litinin cewa daga cikin waɗanda suka rasu akwai mace ɗaya da yara bakwai.

kwale-kwale
Kwale-kwale. Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Shehu ya ƙara da cewar mutanen na kan hanyarsu ta zuwa ɗebo ruwa a wani rafi kusa da Gusau a yayin da kwale-kwalen da ke ɗauke da su ya kife.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Aika Ɗaya Cikin Mutanen Da Suka Sace Ya Siyo Musu Fetur A Neja

Sama da mutane 20 ne a kan kwale-kwalen

Ya kuma bayyana cewa ya zuwa lokacin da ake hirar da shi, an samu nasarar gano wasu daga cikin gawarwakin mutanen da suka mutu a yayin da kuma ake ci gaba da nemo sauran da ke kan kwale-kwalen.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“Mun ceto mutane huɗu da ransu, mun kuma tsamo takwas da suka mutu.”
“Har yanzu muna ta ƙoƙarin nemo ƙarin waɗanda suka mutu saboda akwai sama da mutum 20 a kan kwale-kwalen.”

Ya kuma kirayi gwamnatin jihar ta Zamfara da ta samar da wadataccen ruwa a garin na Gusau domin tun kusan satin da ya wuce akwai ƙarancin ruwan sha a garin.

A rahoton da Daily Nigerian ta wallafa, haɗarin ya faru ne sakamakon cikawa kwale-kwalen lodi fiye da yadda ya kamata ya ɗauka.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Tare Hanya Cikin Dare, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

Ba ruwa suka je ɗebowa ba

Sai dai Kwamishinan ruwa na jihar ta Zamfara Ibrahim Isa, ya shaidawa Punch ta wayar tarho cewa an riga da an magance matsalar ruwa a cikin garin.

Haka nan kuma ya musanta batun da Shehu ya yi na cewar mutanen da suka kife a kwale-kwalen, ruwa za su je ɗebowa.

An shiga zaman zullumi a wasu kauyukan Katsina

A wani labarin kuma, an shiga zaman dar-dar a wasu kauyukan jihar Katsina da ke makwabtaka da jihar Zamfara.

Hakan dai ya biyo bayan rahoto da aka samu na bullar barayin dajin da suka yo gudun hijira daga farmakin da sojoji suke kai musu a Zamfara zuwa gefen kauyukan dake a kananan hukumomin Batsari da Safana na jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng