Rashin Tsaro: Gwamna Ortom Ya Yi Allah Wadai Da Garkuwa Da Shugaban Karama a Taraba
- Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi Allah wadai da sace shugaban karamar hukumar Takum a jihar Taraba
- An yi garkuwa da Boyi Manga ne a mararrabar da ke tsakanin jihar Benue da Taraba a ranar Lahadi 7 ga watan Mayu
- A karshe ya bukaci jami’an tsaro da su hada karfi da karfe da jihar Taraba don kawo karshen rashin tsaro a yankunan
Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya yi Allah wadai da garkuwa da shugaban karamar hukamar Takum a jihar Taraba, Boyi Manga.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an yi garkuwa da Mista Manga ne a ranar Lahadi 7 ga watan Mayu a mararrabar Benue da Taraba bayan an bindige dan sandan da ke tsaronsa.
Da yake maida martani kamar yadda rahotanni suka tattaro a jawabin da ya fitar wanda kakakinsa, Nathaniel Ikyur ya sanya wa hannu, ya ce abin takaici ne yadda rashin tsaro ya yi kamari a mararrabar jihohin biyu.
Gwamnan ya bukaci jami’an tsaro da ke kula da wannan yanki da su yi kokarin ceto shugaban karamar hukumar lami lafiya ba tare da wani rauni ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan, har ila yau ya umarci shugabannin kananan hukumomin Katsina-Ala da Ukum na jihar da su hada karfi da karfe da jihar Taraba don kawo karshen tashe-tashen hankula a yankin da kuma dakile yaduwar 'yan ta'adda.
Ortom ya kuma bukaci mazauna wadannan yankuna da su rinka kai rahoton duk wani wanda ba su yarda da takunsa ba ga jami’an tsaro don kawo karshen rashin tsaro a jihar da ma sauran sassa na Najeriya
Gwamnan Ortom na Benue Ya Dau Zafi, Ya Yi Wa Shugaba Buhari Kakkausan Martani
A wani labarin, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya soki shugaba Buhari bisa dora laifin rashin tsaron da ake fama da shi a jihar akan gwamnatinsa.
Fadar shugaban ƙasa tace gwamna Ortom ne ke da alhaki kan kashe-kashen da ke aukuwa a jihar Benue, inda ta yi zargin cewa gwamnan ya yi fatali da ƙoƙarin da shugaba Buhari ya yi na shawo kan matsalar.
Jihar Benue na fama da rashin tsaro tun farkon hawan gwamnatin shugaba Buhari a shekarar 2015.
Asali: Legit.ng