Kotun Zaben Shugaban Kasa: Dalilin da Yasa Obi Zai Rasa Tsuntsu Zai Rasa Tarko a Kotu, Primate Ayodele

Kotun Zaben Shugaban Kasa: Dalilin da Yasa Obi Zai Rasa Tsuntsu Zai Rasa Tarko a Kotu, Primate Ayodele

  • Babban faston addinin kirista ya bayyana shawarinsa ga Peter Obi kan batun shari’ar zabe da za a fuskanta a cikin watan nan
  • A cewar Primate, babu wanda ya isa ya hana a rantsar da Bola Ahmad Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu da muke ciki a yanzu
  • Hakazalika, ya fadi yadda Inyamurai da kiristoci a Najeriya ke kin tikitin Musulmi da Musulmi da APC ta yi a bana

Najeriya - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele a ranar Lahadi ya shawarci dan takarar shugaban kasa na Labour, Peter Obi da ya kuji zuwa kotu.

A cewarsa, Allah ne kadai zai hana rantsar da Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, Tribune Online ta ruwaito.

Faston ya bayyana cewa, babu mai iya hana rantsar da Tinubu duk da kuwa tikitin Musulmi da Musulmi na APC ya saba da muradin kiristoci a kasar.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai San Makomar Zaben da Ya Lashe, Kotu Za Ta Fara Hukunci kan Nasarar APC

Peter Obi ba zai ci nasara a kotu ba, inji fasto
Peter Obi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Allah ne kadai zai iya hana rantsar da Tinubu

Babban malamin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da hadiminsa, Oluwatosin Osho ya fitar don ba Obi shawari game da karar da ya shigar na kalubalantar sakamakon zaben 2023, Herald ta tattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:
“Babu wanda zai hana rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu, Allah ne kadai zai hana. Bana goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi, Allah bai amince da hadin ba ga Najeriya.
“Akwai abubuwan da kasar za ta fuskanta game da hakan. Najeriya za ta fuskanci kunci saboda tikitin Musulmi da Musulmi.”

Yankin Inyamurai da kiristoci basa goyon bayan tsarin APC da Tinubu

Faston ya kuma bayyana yadda zaben shekarar na ya kasance da kuma yadda kungiyar kiristoci da na yankin Inyamurai suka nuna rashin amincewa da tsarin APC.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Fadawa Bola Tinubu Alfarmar da Yake Nema a Wajen Gwamnatinsa

Peter Obi dai ya ce ba zai amince da sakamakon zaben da aka gudanar ba, kana ya tafi kotu don kalubalantar sakamakon zaben.

Ban dauko wa Peter Obi lauya daga Rasha ba, inji Obasanjo

A wani labarin, kunji yadda Obasanjo ya karyata batun wai ya yi hayar lauya daga kasar Rasha don kare Peter Obi a gaban kotu.

Wannan na zuwa ne bayan da aka yada cewa, Obasanjo ya dauko wata fitacciyar lauyar da ta fi kowa hadari a duniya.

Ya kuma bayyana cewa, ya kamata mutane su daina yada jita-jita tare da tabbatar da labari kafin a fara gamsuwa dashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.