Babbar Magana: Yawan Wayan da Ya Haura Mintuna 30 a Mako Zai Iya Kai Wa Ga Kamuwa da Hawan Jini

Babbar Magana: Yawan Wayan da Ya Haura Mintuna 30 a Mako Zai Iya Kai Wa Ga Kamuwa da Hawan Jini

  • Bincike ya bayyana alakar yin waya da kuma yadda hakan ke tasirantuwa ga hawan jini da mutane ke kamuwa dashi
  • Binciken masana ya bayyana cewa, yawaita yin wayan da ya haura mintuna 30 a mako na iya kai wa ga samun hawan jini
  • Masanan sun yi fashin baki game da yadda binciken ya kasance da kuma tasirinsa ga duniyar lafiya da fasaha

Beijing, kasar China - Yin wayan sama da mintuna 30 a cikin mako guda na da nasaba da karin kaso 12% na hadarin kamuwa da hawan jini inji binciken masana.

A cewar masanan, wayoyin hannu suna fitar da wani magadisun mitar rediyo takaitacce, wanda ke da danganta da yawaitar hawan jini bayan samun dama na dan gajeren lokaci.

A halin da ake ciki, akalla uku cikin hudu na yawan al’ummar duniya daga shekaru 10 zuwa sama ne ke amfani da wayoyin hannu, rahoton Daily Mail.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Jirgin sama daga Arewa ya kama da wuta, ya yi sauka mai hadari a Abuja

Yawan waya na kai wa a kamu da hawan jini
Binciken masana kan yawaita waya | Hoto: hindustantimes.com
Asali: UGC

Akalla, akwai mutunen da suka mallaki hankalinsu miliyan 1.3 da ke tsakanin shekaru 30 zuwa 79 da ke dauke da cutar hawan jini a duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hawan jini a mahangar lafiyar dan adam

Hawan jini na daya daga manyan hadurran da ke kai wa ga bugawar zuciya da ke kai wa ga mutuwa baktatan ba tare da dogon jinya ba.

Farfesa Xianhui Qin na Jami'ar Kiwon Lafiya ta Kudancin Guangzhou ta kasar China ya ce:

"Lura da yawan mintunan da mutane ke batawa wajen yin magana ta wayar hannu ne ke da muhimmanci ga lafiyar zuciya, inda adadin mintuna da ake batawa ke nufin girman hadarinsa."

Binciken, wanda aka buga a jaridar European Heart Journal-Digital Health, ya kuma nuna cewa idan aka kwatanta da wadanda ke amfani da waya na kasa da mintuna 5 a mako, da masu yin mintuna 30-59, sa'o'i 1-3, sa’o’i 4-6 sa'o'i da fiye da sa'o'i 6, hakan ya nuna hadarin kamuwa da hawan jini a tsakaninsu da 8%, 13%, 16% da 25% bi da bi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Uba Goye Da Dansa Da Tsakar Dare Ya Yadu, Ya Ce Baya Barinsa Ya Yi Bacci

Yadda binciken ya nuna alakar hawan jini da yawan waya

Sai dai, binciken ya bayyana cewa, akwai sauki ga masu amfani da amsa-kuwwa wajen yin waya sabanin wadanda ke karawa a kunne wajen hadarin kamuwa da hawan jinin, cewar New York Post.

Ya kara da cewa:

“Binciken da muka yi ya nuna cewa yawan yin wayar ba zai yi tasiri a kan hadarin kamuwa da cutar hawan jini ba matukar dai ba a haura rabin sa’a a mako ba, ana bukatar karin bincike don tabbatar da sakamakon, amma ya zuwa yanzu yana da kyau a rika waya daidai kima.”

Don bincika alakar da ke tsakanin yawan waya da hawan jini, binciken ya hada jumillar mutane 2,12,046 masu shekaru 37 zuwa 73 da basu da hawan jini.

A baya, rahoton da muka tattaro ya bayyana irin kura-kuran da mutane ke yi wajen cajin wayoyinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.