"Yar'adua Bai Taba Son Yin Siyasa Ba", Hajiya Turai Ta Bayyana Abinda Mijinta Ya So Yi a Rayuwa
- Uwargidan tsohon shugaban ƙasa, Umaru Musa Yar'adua, tace baya da burin yin siyasa a rayuwar sa
- Hajiya Turai ta bayyana cewa Yar'adua burin sa shine ya zama malamin makaranta ba siyasa
- Turai ta kuma bayyana cewa har yanzu tana tunawa da tsohon mijin na ta, sannan ta yi kewar sa
Jihar Katsina - Uwargidan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Umar Musa Yar'adua, Hajiya Turai, ta bayyana cewa ƙaddara ce ta sanya mijinta ya zama shugaban ƙasa.
Daily Trust ta kawo rahoto cewa, uwargidan ta bayyana cewa mijinta bai taɓa rasa barci ba domin ganin sai ya zama shugaban ƙasa.
Da take magana a wata hira da BBC Hausa, kan cikar shekara 13 da rasuwar mijin na ta, Hajiya Turai, ta bayyana cewa mjinta bai taɓa son siyasa ba, inda ta ce za ta iya kiran sa da wanda ya shiga siyasa bisa ƙaddara.
A kalamanta:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Babban burin sa a rayuwa shine ya zama malamin makaranta, ya dawo gida daga makaranta ya yi ta raha har wayewar wata rana. Bai taɓa son siyasa ko mulki ba, amma Allah ya sanya ya shiga siyasa sannan har ya zama shugaban ƙasa."
"Duk da yana shugaban ƙasa, a lokacin bai sauya rayuwar sa ba. Bai taɓa kwaikwayon tsadaddiyar rayuwa sannan ya yi rayuwar sa a matsayin mutum mai sauƙin kai."
Hajiya Turai ta kuma bayyana cewa kullum tana tunawa da Yar'adua sannan tana matuƙar kewar mijin na ta.
"Ina tunawa da Yar'adua kullum ba sai kawai a ranar tunawa da shi ba. Ina tunanin shi sannan ina kewar sa a kullum." A cewarta.
Da take magana kan gwamnati mai jiran gado ta Bola Tinubu, Hajiya Turai ta buƙaci uwargidan shugaban ƙasa mai jiran gado, Remi Tinubu, da ta zama mai haƙuri da juriya domin abinda ke gabanta abu ne mai matuƙar wahala.
Turai ta kuma ƙara da cewa tana da tabbacin cewa Remi Tinubu za ta iya jure duk wasu ƙalubale da za ta iya fuskanta sannan ta taimakawa mijinta wajen sauke nauyin da ke kan sa.
Turai ’Yar Adua Ta Siffinta Halin Mijinta Shekaru 13 Bayan Mutuwarsa
A wani rahoton na daban kuma, Hajiya Turai ta bayyana wasu kyawawan halaye na marigayi Umaru Musa Yar'adua.
Hajiya Turai ta bayyana Umaru a matsayin mutum mai sauƙin kai wanda bai damu da abun duniya ba.
Asali: Legit.ng