Gwamma Ayade Ya Kakaba Dokar Zaman Gida a Garruruwan Kuros Riba
- Gwamnan jihar Kuros Riba ya koka da abinda ya faru, ya ƙaƙaba dokar zaman gida a yankuna biyu da rikice ya ɓarke a jihar
- Dokar zata riƙa aiki daga karfe 6:00 na dare zuwa karfe 6:00 na safiyar kowace rana har sai komai ya lafa a yankunan
- Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda aka rasa rayuka da dukiyoyi, ya sha alwashin hukunta duk wanda aka gano yana da hannu
Cross River - Gwamnan jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade, ya kaƙaba dokar kulle daga karfe 6:00 na dare zuwa 6:00 na safiya a garuruwan Oyonum da kuma Ofatura.
Channels tv ta rahoto cewa gwamna Ayade, mamban jam'iyyar APC, ya sanya dokar zaman gida a garuruwan 2 da ke ƙaramar hukumar Obubura kuma zata fara aiki nan take.
Wannan na zuwa ne biyo bayan tashin hankali da ke faruwa na faɗa tsakanin al'umma mazauna garuruwan guda biyu.
Mai baiwa gwamna shawara ta musamman kan harkokin midiya da yaɗa labarai, Christian Ita, ne ya tabbatar sanya dokar zaman gidan a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce gwamnatin jihar Kuros Ribas ta umarci hukumomin tsaro su mamaye garuruwan kuma su tabbata jama'a sun yi ɗa'a ga dokar zaman gidan da aka sanya.
Gwamna Ben Ayade ya ƙara da cewa dokar wacce zata riƙa aiki daga 6:00 na dare zuwa 6:00 na safe zata fara aiki kan mazauna yankunan nan take babu ɓata lokaci.
A rahoton The Cable, Sanarwan ta ce:
"Mai girma gwamna ya umarci hukumomin tsaro su tabbata al'umma da ke yankunan da dokar kullen ta shafa sun yi biyayya sun zauna a gida a tsawon lokacin."
"Gwamnan ya kuma koka kan rasa rayuka da dukiyoyi a sabon rikicin da ya ɓarke tsakanin yankunan biyu, kuma ya lashi takobin cewa gwamnatinsa zata zakulo duk masu hannu a tada rikicin."
Babbar kasuwa a Najeriya ta kama da wuta
A wani labarin kuma kun ji cewa Fitacciyar Kasuwar Kasa da Kasa a Najeriya Ta Kama da Wuta
Lamarin daiya haddasa ruɗani da tashin hankali kuma matasa sun hana ma'aikatan kashe gobara shiga wurin su gudanar da ayyukansu.
A wata sanarwa da daraktan hukumar kashe wuta da ayyukan ceto ta jihar Legas ta fitar, ta ce zuwa yanzu sun haɗa kai da hukumomin tsaro don shawo kan lamarin.
Asali: Legit.ng