'Yan Sanda Sun Cafke Wani Basarake a Jihar Arewa Mai Rura Wutar Rikici
- Ƴan sanda a jihar Bauchi sun cafke wani basarake a jihar kan zargin tayar da hargitsi da rura wutar sa
- Rikici dai ya ɓarke ne biyo bayan wani naɗin sarauta da basaraken ya yi wanda bai yi wa wasu matasa daɗi ba
- An dai cafke basaraken ne tare da wasu mutum shida waɗanda ake zargin da hannun su dumu-dumu a rikicin
Jihar Bauchi - Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da cafke zaɓaɓɓen basarake mai riƙe da sarautar Gum Zaar na ƙauyen Sayawa a jihar Bauchi, mai ritaya Air Commodore Ishaku Komo, mai shekara 71 a duniya.
Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa ƴan sandan sun cafke basaraken ne tare da wasu mutum 6, kan zargin aikata laifukan da suka haɗa da tayar da hargitsi, rura wutar rikici, raunata wasu da kisan kai.
Sauran mutanen da aka cafke tare da basaraken sun haɗa da Matthew Ishaya mai shekara 56, Yakubu Bala mai shekara 65, Appolos Hassan mai shekara 72.
Sauran sune Nathaniel Joshua, mai shekara 40, Abenagu Zakka mai shekara 30 da James Dajum mai shekara 65.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Ahmed Wakili, ya fitar, ya bayyana cewa an cafke basaraken ne kan rikicin da ya ɓarke kan taƙaddamar naɗin sarauta, saɓanin jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kama shi ne saboda bambancin addini.
Kakakin ya ce rikicin ya fara ne bayan Ishaku Komo ya naɗa wani Mr Matthew Ishaya a matsayin dagacin ƙauyen Sang cikin ƙaramar hukumar Bogoro.
Wannan naɗin sarautar da aka yi ya fusata matasa waɗanda suka fito, zanga-zanga wacce daga ƙarshe ta rikiɗe ta koma rikici, wanda ya janyo asarar dukiya da rai, cewar rahoton Independent.
SP Ahmed Wakili, ya ce an samu bindiga, gidan harsashi da wuƙa guda ɗaya a hannun waɗanda ake zargin.
Ya kuma bayyana cewa ana cigaba da gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin abubuwan da suka auku.
Basaraken Da Kotu Ta Tsige Daga Kan Karagar Mulki Ya Mutu a Ondo
A wani labarin na daban kuma, wani babban basarake da aka tuɓewa rawanin sa, ya rig mu gidan gaskiya a jihar Ondo.
Oba Lawrence Oluwole Babajide, ya koma ga mahaliccin sa yana da shekara 92 a duniya.
Asali: Legit.ng