Basaraken Da Kotu Ta Tsige Daga Kan Karagar Mulki Ya Mutu a Ondo

Basaraken Da Kotu Ta Tsige Daga Kan Karagar Mulki Ya Mutu a Ondo

  • Allah ya yi wa Oluoke na masarautar Okeigbo da ke karamar hukumar Ile-Oluji/Okeigbo, a jihar Ondo, Oba Babajide rasuwa
  • Kafin rasuwarsa babbar kotun jihar Ondo ta tsige shi daga kan karagar mulki saboda ba ɗan gidan Sarauta bane
  • Yariman masarautar ya ce tuni aka fara shirye-shirye binne marigayin domin ya tafi cikin salama

Ondo - Sarkin masarautar Okeigbo da ke ƙaramar hukumar Ile-Oluji/Okeigbo a jihar Ondo, kudu maso yammacin Najeriya, Oba Lawrence Oluwole Babajide, ya riga mu gidan gaskiya.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Sarkin, wanda sunan sarautarsa, Oluoke na Okeigbo, kuma ana masa laƙabi da 'Bamigbala na I' ya mutu yana ɗan shekara 92.

Oba Babajide.
Basaraken Da Kotu Ta Tsige Daga Kan Karagar Mulki Ya Mutu a Ondo Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Kotu ta tsige Marigayin tun yana da rai

Legit.ng Hausa ta gano cewa a watan da ya gabata, babbar kotun jihar Ondo ta tsige marigayi Oba Babajide daga kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

DCD Ta Gano Makarkashiyar da Ahmad Lawan Suke Shiryawa Kafin Zaben Majalisa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kotu ta ɗauki wannan mataki ne kasancewar Basaraken ba ɗan gidan Sarautar Aare Kugbaigbe na Okeigbo ba?2, kuma gidan ne ke da alhakin samar da sabon Sarki a shekarar 2018.

Sai dai Oba Babajide bai gamsu da hukuncin da Kotun ta yanke ba, sakamakon haka ya ɗaukaka kara zuwa gaba gabanin rai ya yi halinsa.

Yasuhe Sarkin ya kwanta dama?

Baba Loja na masarautar Okeigbo, Chief Akinbobola Adedigbo, ne ya sanar da rasuwar basaraken a babbar kasuwar garin da safiyar Jumu'a 5 ga watan Mayu, 2023.

Haka zalika a wata sanarwa da mai magana da yawun fadar sarkin, Yarima Alexander Omojadegbe, ya fitar, ya ce tuni waɗanda ke da alhaki suka fara shirye-shiryen jana'iza.

Ya ce tuni mahukuntan fada suka fara duk wani shiri da ya dace na binne mamacin domin ya tafi cikin salama.

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Ko Obi? Tsohon Shugaban Kasa Ya Roki Alfarma 1 Wurin Yan Najeriya Kan Shari'ar Zaben 2023

Marigayi Oba Babajide ya kasance Oluoke na Okeigbo na 6 a tarihin kafuwar Masarautar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Fitacciyar Kasuwar Kasa da Kasa a Najeriya Ta Kama da Wuta

A wani labarin kuma Kun ji cewa ibtila'in gobara ya afka wa shahararriyar kasuwar Ƙasa da kasa da ke jihar Legas

Rahotanni sun nuna cewa kasuwar da ke ƙaramar hukumar Ojo ta kama da wuta yau Jumu'a 5 ga watan Mayu, 2023.

Hukumar kashe gobara da ayyukan ceto ta jihar Legas ta tabbatar da lamarin, ta ce tuni jami'ai suka fara kokarin shawo kan wutar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262