Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Basaraken Da Ya Yi Barazanar Kawo IPOB Legas
- Kotu da ke zamanta a Sabo a jihar Legas ta bai wa Shugaban kabilar Ibo a Legas, Eze Fredrick Nwajagu beli
- Wanda ake zargin a baya ya sha alwashin kawo kungiyar ‘yan ta’addan IPOB zuwa jihar don kare kabilarsa dake jihar
- Shugaban kotun, Peter Nwaka shi ne ya bada belin da taran N1m da kuma shaidu guda 4 da ke da zaunannun kadarori a jihar
Jihar Legas - Wata kotu da ke zamanta a Sabo a yankin Yaba a jihar Legas ta bada belin shugaban kabilar Ibo mazauna Ajawo a jihar, Fredrick Nwajagu wanda ya yi barazanar.
An tusa keyar Fredrick ne zuwa kotu bisa zarginsa da ake na alwashin kawo ‘yan ta’addan IPOB cikin jihar Legas a hirarsa da ya yi gidan talabijin na Channels.
Babban mai shari’a a kotun, Peter Nwaka shi ne ya bada belin da taran N1m da kuma shaidu guda 4.
Ka’idojin bada belin
Rahotanni sun tattaro cewa kotun ta ce dole shaidun su mallaki kadarori da aka musu rijista da kuma kawo takardun kotu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan wanda ake kara, Nkechi Agubuzor ya nemi kotun da tayi adalci a hukuncin da kuma rokan kotun da bai wa wanda ake zargin beli.
A karshe dai mai shari’a Nwaka ya ba da belin wanda ake zargin bayan karanto masa laifukansa.
Gwamnati Najeriya Ta Caccaki Kasashen Turai da Ke Daukar Nauyin ’Yan Ta’addan IPOB
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta caccaki wasu kasashen yammacin duniya da ke ba kungiyar ta’addancin nan ta IPOB tallafi wajen gudanar da barnarta.
Wannan na fitowa ne daga bakin ministan yada labarai da al’adu na kasar, Lai Muhammad a lokacin da yake magana a birnin Washigton DC na Amurka, Daily Trust ta ruwaito.
Kungiyar Ibo Ta Najeriya Ta Ragargaji Gwamnatin Buhari Kan Hukuncin Ekweremadu, Ta Bayyana Mataki Na Gaba
A cewar Ministan, lamarin tallafawa IPOB ba komai bane face tsagwaron munafunci na yammacin duniya, tare da ikrarin suna yakar ta’addanci, amma a zahiri kara rura wutar rikici suke ta hanyar ba kungiyoyin ta’addanci kamar IPOB kudade.
Najeriya dai na fama da tashin hankula da bangarori da dama a kasar ciki har da yankin Arewan kasar da ke fama hare-haren 'yan bindiga musamman Arewa maso yamma.
Asali: Legit.ng