Yanzu-Yanzu: Kamfanonin Jiragen Saman Jigilar Maniyyatan Bana Sun Ki Sanya Hannu Kan Abu 1

Yanzu-Yanzu: Kamfanonin Jiragen Saman Jigilar Maniyyatan Bana Sun Ki Sanya Hannu Kan Abu 1

  • Kamfanonin jiragen saman da za su yi jigilar maniyyata hajjin bana sun kawo tsaiko wajen sanya hannun a yarjejeniyar su da NAHCON
  • Kamfanonin sun ki yarda su sanya hannu a yarjejeniyar su da hukumar NAHCON domin jigilar maniyyata hajjin bana
  • Rashin sanya hannun su a yarjejeniyar yana da nasaba da rikicin da ake yi a ƙasar Sudan

Abuja - Kamfanonin jiragen sama na cikin gida Najeriya, da aka zaɓa domin jigilar Alhazan bana na shekarar 2023, sun ƙi yarda su sanya hannu kan yarjejeniya da hukumar jindaɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON), saboda rikicin Sudan.

Jaridar Daily Trust tace wakilan kamfanonin jiragen saman da suka ƙi rattaɓa hannu, sun haɗa da Azman Air, Max Air, Air Peace da Aero Contractors.

Kamfanonin jiragen saman da za su yi jigilar maniyyatan bana sun ki sanya hannu
Wasu maniyyata na kokarin shiga jirgi Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Rattaɓa hannun kan yarjejeniyar jigilar mahajjatan, yau yakamata a yi ta, amma an ɗage ta har zuwa ranar Talata mai zuwa saboda kamfanonin sun buƙaci a basu lokaci su yi shawara da manyan su.

Kara karanta wannan

Shiri Ya Kwabe: Jigon Jam'iyya Ya Garzaya Kotu Neman a Dawo Masa Da Kayayyakin Da Ya Raba Lokacin Zabe

Sai dai kamfanin jirgin saman ƙasar waje guda ɗaya tilo kawai a cikin su, Fly Nas, ya rattaɓa hannu kan yarjejeniyar, inda aka ware masa sama da maniyyata 28,000, wanda hakan na nufin ya samu kaso 40% na Alhazan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kulle sararin samaniyar Sudan da aka yi saboda rikicin da ake gwabzawa a ƙasar, zai shafi maniyyatan da suka fito daga yankin Afrika ta Yamma, saboda itace hanya mafi gajarta domin zuwa ƙasar Saudiyya a wajen su. 

A yayin da aka rattaɓa yarjejeniyar farko tsakanin kamfanonin da hukumar NAHCON, bi ta wata hanyar zai zo da tsada sannan yana buƙatar a sake waiwaye kan kuɗin da maniyyatan za su biya.

Hukumar NAHCON a cikin wata Afirilu, ta sanya ƙarancin kuɗin kujera a matsayin N2.88m sannan mafi yawan kuɗin kujera a matsayin N2.9m, wanda daga baya aka ƙara ya kai N3.2m.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Matashin Saurayi Ya Burma Wa Mahaifiyarsa Wuƙa Har Ta Mutu a Kano

Hukumar Alhazai Ta Sanya Wa'adin Kammala Biyan Kudin Hajjin Bana

A baya rahoto ya zo kan yadda hukumar Alhazai ta sanya ranar kammala biyan kuɗin hajjin bana.

Hukumar tace duk maniyyacin da bai biya kuɗin sa ba, a wa'adin da ta sanya ba, zai iya samu gagarumar matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng