“Ina So Ta Tafi”: Matashiya Ta Koka Yayin da Mahaifiyarta Ta Ziyarci Gidanta Ba Da Son Ran Mijinta Ba

“Ina So Ta Tafi”: Matashiya Ta Koka Yayin da Mahaifiyarta Ta Ziyarci Gidanta Ba Da Son Ran Mijinta Ba

  • Wata matashiya yar Najeriya ta caccaki mahaifiyarta da ta haifeta kan kokarin da take yi na kashe mata aure
  • A cewar matashiyar, mijinta ya haramta mata kawo kowani danginta gidan aurensu
  • Sai dai kuma, mahaifiyarta ta kawo masu ziyarar bazata, kuma tun daga lokacin aurenta ke rawa yayin da mijin ya canja mata

Wata matashiya yar Najeriya ta sha alwashin cewa ba za ta taba yafewa mahaifiyarta da ta tsuguna ta haifeta ba idan har aurenta ya mutu.

A cewar matashiyar, mijinta ya gindaya sharadi cewa kada wani daga cikin danginta ya ziyarci gidansu bayan aure.

Wasu mata a tsaye cikin damuwa
“Ina So Ta Tafi”: Matashiya Ta Koka Yayin da Mahaifiyarta Ta Ziyarci Gidanta Ba Da Son Ran Mijinta Ba Hoto: @Pius Utomi, Ekpei
Asali: Getty Images

Sai dai kuma, suna zaune kwatsam sai mahaifiyar matar ta kawo masu ziyarar bazata, kuma hakan ya haddasa rikici a gidanta.

Mijinta ya daina cin abincinta kuma tun daga lokacin da mahaifiyarta ta isa gidan, bai sake cewa uffam da ita ba.

Kara karanta wannan

Bani da ko saurayi: Budurwa ta ce tallan gwanjo na kai mata, ta sayi motar N36m

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan hakan, matar ta bukaci mahaifiyarta da ta bar mata gidan aurenta, amma ta yi watsi da ita. Ta yi alkawarin cewa ba za ta taba yafewa mahaifiyarta ba idan aurenta ya mutu.

Princess Chidimma Okonkwo ce ta wallafa labarin mai tsuma rai a Facebook.

Jama'a sun yi martani

Chiamaka Peace ta ce:

"Dan Allah dukkanku da kuke gidan nan baku da hankali, robar fentin gari ya zama 1500 yanzu."

Nnenna Udu ta rubuta:

"Mahaifiyar nan tata tana bukatar lambar yabo ma. Ta yaya ta iya zama a inda ba a sonta ne ma? Iyaye da dama za su karanci alamu sannan su wuce da kansu."

Chinenye Mbelu ta rubuta:

"Ki yi abun da zuciyarki ta raya maki, wani irin shawara kike so? Kawai ki yi wa mahaifiyarki abun da kike so diyarki ta yi maki. Shikenan magana ta kare."

Kara karanta wannan

“Wayyo Allah Ni Cokali Ce?” Bidiyon Kyautar Tsaleliyar Mota Da Saurayi Ya Yi Wa Budurwarsa Ya Dauka Hankali

Chisom Enye ta yi martani:

"Dukkanku baku da tunani, mijinki da ke gaba dake, da ke da kike so mahaifiyarki ta wuce da ita mahaifiyarki da ta zo ba tare da ta sanar ba."

Remi Balogun ta ce:

"Kan ki na bukatar a duba kwakwalwarki. Ya yi maki kyau da kika zabi uwar mijinki a matsayin uwarki. Wani irin mutum mara tausayi ne kika aura?"

Bana bukatar saurayi, matashiya ta magantu, ta ce yayanta ya isheta komai

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta bayyanawa duniya cewar bata bukatar kowani da namiji da sunan saurayi a rayuwarta domin yayanta ya gama mata komai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng