Bani da Miji: Budurwa Mai Shekaru 21 da Ke Sayar Gwanjo Ta Sayi Motar Miliyan 36

Bani da Miji: Budurwa Mai Shekaru 21 da Ke Sayar Gwanjo Ta Sayi Motar Miliyan 36

  • Wata matashiya da ke siyar da gwanjo don dogaro da kai ta magantu akan kasuwanci da kudaden da take samu
  • A cewar matashiyar mai kwazon nema, sana’ar na da riba sosai domin tana samun miliyoyin nairori
  • A bidiyon da ya yadu, ta bayyana cewa ta siya motar da ya kai miliyan N36 da sana’ar
  • Wata matashiya yar Najeriya mai suna Amaka ta bayyana yadda ta ke samun miliyoyin naira da sana’ar gwanjo.

A wani bidiyo da Mc Mbakara ya wallafa a Facebook, matashiyar ta ce ta siya motar da farashinta ya kai naira miliyan 36 sannan ta karbi hayar gida na naira miliyan 9.

Da aka tambaye ta a kan kasuwancinta, ta ce ta karanci dabarun da zai yi mata aiki.

A cewarta, ta yi amfani damar soshiyal midiya sannan tana tallata haajarta a intanet inda ta tara kwastamomi da yawa.

Kara karanta wannan

Karya kike: Bidiyon yadda yarinya ta fashe da kukan haushin ta ci maki 259 a JAMB

Budurwa mai tallan gwanjo ta sayi motar N36m
Budurwar mai sana'ar gwanjo a jikin motarta | Hoto:MC Mbakara
Asali: Facebook

Ta kuma nanata cewa ita mace ce mai yanci wacce bata dogara da wani da namiji don daukar dawainiyarta ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalamanta:

“Shekaruna 21. Farashin motata miliyan N36. Ni yar kasuwa ce. Ina siyar da kayan gwanjo. Masu kyau. Mutum na samun na tattare da dabarun da ka yi amfani da shi ne. Kasuwancin yanar gizo ne a zahirin gaskiya. Ba kowa ne ya san yadda ake kula da kasuwancin yanar gizo ba.
“Ya zama dole ka samo dabaru masu kyau da za su dace da kasuwancin ka da kudaden da kake samu. Ina zama ne a Lekki. Ina Biyan naira miliyan 7 duk shekara a matsayin kudin haya. Gaba daya harda kudin chaji naira miliyan 9.
“A wannan karnin, matasa da dama basa son ci da guminsu. Ina son yin magana ne musamman a kan mata. Ya kamata ki kasance da dabaru kan aikinki. Duk abun da kike yi, ki tabbata ya banbanta da na kowa.

Kara karanta wannan

“Wayyo Allah Ni Cokali Ce?” Bidiyon Kyautar Tsaleliyar Mota Da Saurayi Ya Yi Wa Budurwarsa Ya Dauka Hankali

“Ina mamakin dalilin da yasa kuke mamakin cewa na mallaki motar miliyan N36 ta hanyar siyar da gwanjo. Dabaruna na yi mani aiki har na kai inda nake a yanzu. Bani da saurayi. Ina da yanci sosai. Ni da kaina nake biyawa kaina bukatuna.”

Jama’a sun yi martani

Tombari Tonwe ta ce:

“Mbakara, dan Allah ina so na bar aikina na fara siyar da gwanjo, idan dabaru ne, za ki taimaka ki hada ni da Amaka, na koyi dabara. Ban san cewa sana’ar gwanjo na da riba ba.”

Williams Talent ya ce:

“Sana’ar gwanjo da yake gadon gidanmu, shine sana’a na farko da na fara gani lokacin da na zo duniyar nan.
"Ji fa yarinyar da ba shigo da su take yi ba sinki daya take siya tana tsayawa a rana tana ihu ita ta siya irin motar nan wanda ko ni da nake shigo da su ba zan iya yin wannan karyar ba.

Kara karanta wannan

Garin dadi: Mata ta bar Najeriya, yadda ake siyar da daurin tuwo 1 N920 ya bata mamaki

2Yallabai kawo ta nan aba dan Allah ta wayar mana da kai kan dabarun da take amfani da su wajen siyar da nata gwanjon dan Allah yana da muhimmanci a garemu. kawo ta.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng