Jiragen Yaki Marasa Matuka Sun Kai Hari Fadar Shugaban Kasar Rasha

Jiragen Yaki Marasa Matuka Sun Kai Hari Fadar Shugaban Kasar Rasha

  • Wasu jirage marasa matuƙa sun yi yunkurin kai hari fadar shugaban ƙasar Rasha amma ba su kai ga nasara ba
  • Rasha ta zargi ƙasar Ukraine da wannan yunkuri da nufin ganin bayan shugaba Vladimir Putin
  • Amma a bangarenta, Ukraine ta nesanta kanta da hannu a lamarin, inda ta ce a yanzu ta fi maida hankali wajen ƙwato yankunanta

Rahotanni daga kasar Rasha sun nuna cewa wasu jirage marasa matuƙa guda biyu sun kai hari kan fadar shugaban ƙasa da ke Kremlin a cikin dare amma ba su samu nasara ba.

Jaridar Aminiya ta tattaro cewa ƙasar Rasha ta zargi abokiyar faɗanta, Ukraine da ƙulla kai harin na Bam, da nufin ganin bayan shugaban ƙasa, Vladimir Putin.

Putin.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, yana jawabi Hoto: Vladimir Putin
Asali: Getty Images

Rahoton kafar watsa labarai ta ƙasar Rasha RIA ya nuna cewa sa'ilin da jiragen suka yi yunkurin kai harin, Shugaba Putin ba ya cikin fadar Kremlin, yana gidansa na Novo Ogaryovo.

Kara karanta wannan

"Na Yi Nadamar Mulkin Buhari Saboda Manyan Abu 2 da Ya Kawo" Tsohon Makusancin Buhari Ya Tona Asiri

Ta kuma ayyana wannan yunkuri da, "Barazana ga rayuwar shugaban ƙasa Putin gabanin zuwan ranar 9 ga watan Mayu, da ake sa ran zai halarci faretin nasara."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya, ya hasko yadda wani abu ke shawagi a saman fadar shugaban Rasha amma daga bisani kuma ya tarwatse.

Kasar Ukraine ta maida martani

Amma a ɓangarenta, ƙasar Ukraine ta musanta kai hari fadar Kremlin da cewa babu abinda zai sa ta kai hari da jirage marasa matuƙa.

Kakakin shugaban Ukraine ya bayyana cewa a halin da ake ciki yanzu, sun maida hankali ne wajen ganin yankunan da Rasha ta kwace sun dawo hannunsu.

Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa tuni Rasha ta lalata jiragen biyu amma ta ce ya zama tilas ta shiryawa duk wani yunkuri da ƙasar Ukraine ka iya yi nan gaba.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Babban Lauya Ya Ba Wa APC Da Yan Najeriya Muhimmin Shawara Kan Kujerar Kakakin Majalisa

Haɗarin mota ya yi ajalin Malamai uku a Ekiti

A wani labarin kuma Wasu Malamai Uku da Karin Mutum Daya Sun Mutu a Hadarin Mota a Ekiti

Malaman coci watau Fastoci 3 sun mutu a wani mummunan haɗarin mota da ya rutsa da su a jihar Ekiti, kudu maso yammacin Najeriya.

Rahoto ya nuna Fastoci 2 sun rako ɗaya zuwa sabon cocin da aka maida shi amma ibtila'in ya rutsa da su kuma nan take rai ya yi halinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262