“Baki da Godiyar Allah”: Yarinya Ta Ci 259 a JAMB, Ta Fashe da Kuka Don Makin Ya Mata Kadan
- Wata dalibar sakadare ta shiga jimami yayin da ta bar ‘yan soshiyal midiya baki bude kan sakamakon jarrabawarta na UTME
- Yarinyar ta sharbi kuka ainun, tana ta bayyana bacin rai bayan da ta samu maki 259 a jarrabawar da ta rubuta
- Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun bayyana fushi, inda wasu ke ce mata bata da godiyar ubangiji
Wata yarinya ‘yar Najeriya ta sharbi kuka bayan da ta duba sakamakon jarrabawarta na UTME da hukumar JAMB ke shiryawa.
Yayin da wata mata ke kokarin rarrashinta, yarinyar ta ci gaba da kuka inda take mamakin ya aka yi ta ci 259 a jarrabawar.
Bidiyon yarinyar da aka yada a kafar TikTok ya jawo cece-kuce da martanin jama’a da yawa kan halin yarinyar.
Mutane da yawa sun caccaki yarinyar da kuma kiranta wacce bata da godiyar Allah inda suka ce wasu basu samu maki irin nata ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a a kafar sada zumunta
Deevoo18:
“Zan ma zagi wanda ke rarrashinta ta... idan taga dama ta ruga da gudu ta shiga daji...”
Tommy:
“Kalli wannan fa kuka kike don kin samu 259 wanda ya samu 110 kawai ya mutu kenan.”
blessingabraham432:
“250 nake ji ne ko kuma kunnuwa basa ji da kyau ne.”
AshabiAde:
“259 za ki iya kokari a shekara mai zuwa.”
tao_coco:
“Ya zaki yi dani da na samu 167 bara kuma yanzu bana jami’ar.”
Beezee_Jnr:
“Wannan wasa kike ma, ni da na samu 180 sai sadaka nake ta yi.”
Somi:
“Meye mu kuma da muka samu 140 za mu yi kenan.”
user3826571751545:
“Dakata, 250 amma kina kuka. Allah ina rokonka.”
An saki sakamakon jarrabawar UTME na bana
A baya kunji yadda hukumar shirya jarrabawa ta JAMB ta bayyana sakin sakamakon jarrabawar UTME da aka rubuta a makon da ya gabata cikin watan Afrilu.
Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bayyana sakamakon jarrabawar, inda dalibai ke bayyana adadin makin da suka samo a jarrabawar ta shiga manyan makarantun gaba da sakadare.
Rahoton da muka samo a baya ya bayyana yadda kowa zai iya bude sakamakon jarrabawar ta wayar salulu ta hannu ba tare da wata matsala ko jigila ba.
Asali: Legit.ng