An Kori Tsohon Shugaban APC Na Jigawa Tare da Tsare Shi Bisa Laifin Sukar Gwamna Badaru

An Kori Tsohon Shugaban APC Na Jigawa Tare da Tsare Shi Bisa Laifin Sukar Gwamna Badaru

  • Jam’iyyar APC ta kori shugabanta a jihar Jigawa bisa laifin shiga idon gwamnan Mohammed Badaru Abubakar
  • An kama shugaban APC da wani mutum bayan da aka zarge su da sukar gwamna a gidan rediyo a jihar
  • ‘Yan sanda sun tabbatar da kamun, sun bayyana gaskiyar laifin da jiga-jigan na APC suka aikata

Jihar Jigawa - Shugaban jam’iyyar APC na jihar Jigawa, Alhaji Habibu Sani Sara da wani mutum sun gamu da fushin hukumar bisa umarnin gwamnan jihar, Mohammed Badaru Abubakar.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan sanda sun kama Sara ne tare da wani bayan da aka dakatar dashi daga shugabancin jam’iyyar.

Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa, hakan ya faru ne bayan da aka zargi shugaban da tofa kalaman da basu dace ba kan gwamnan jihar.

Gwamnan jigawa ya sa an kama shugaban APC
Jihar Jigawa da ke Arewa maso Yamma | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar majiya, Sara da wasu sun zargi gwamnan ne da kokarin kakaba wa gwamna mai jiran gado ala-ka-kai na yawan ayyukan da aka bayar bayan aski ya zo gaban goshi.

Kara karanta wannan

Atiku ne ya lashe zabe: PDP ta caccaki ministan Buhari, ta tono barnar APC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An kori shugaban APC da wani babban jigon jam’iyyar

Hakazalika, an dakatar da shugaban na APC, Sara da kuma Habu Karami Jahun, wani jigon jam’iyyar bisa zarginsu da gangamin sukar algadarin gwamnan.

‘Yan sanda daga nan suka kwamushe su bayan gudanar da wani shirin gidan rediyo na kai tsaye game da ayyukan gwamnan, rahoton Crime Channels.

A yayin shirin, ‘yan siyasan biyu sun zargi gwamnan da ba da wasu ayyukan kwangila da suka hada da siyan wasu motoci 200 da amfaninsu bai bayyana a fili ba.

Sun kuma zarge shi da kokarin ci gaba da jan ragamar gwamnatin jihar bayan 29 ga watan Mayu ta hanyar kakaba wasu mambobin majalisarsa ga gwamna mai jiran gadi, Malam Umaru Namadi.

‘Yan sanda sun tabbatar da halin da ake ciki

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da gayyatar ‘yan siyasan biyu tare da tsare su bayan samun korafi daga na kusa da gwamna, Malam Habibi Ringim.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jirgin Shugaban Kasa Ya Lula Kasar Waje Domin Samun Gyara Na Musamman

A martaninta ga lamarin, jam’iyyar APC a karamar hukumar Gwaram ta tabbatar da korar Alhaji Habibi Sani Sarea da wani Tukur Fagam.

Korar ta su na dauke da sa hannun Alhaji Ayuba Umar Nasara, inda yace korar tasu za ta zama izina ga sauran ‘yan jam’iyyar.

A baya, kunji yadda aka kori shugaban APC a jihar Edo bisa wasu dalilai da suka shafi siyasar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.