Ranar Ma'aikata ta Duniya: Muhimman Abubuwa Bakwai Game Da Ranar 1 Ga Watan Mayu
Ana bikin ranar ma'aikata ta duniya, da kuma ake kira da ranar kwadago, ranar 1 ga watan Mayu kowace shekara don jinjina ga ma'aikata a fadin duniya.
Yayin da Najeriya ta bi sahun kasashen duniya don bikin murnar ranar ma'aikata ta 2023, ga wasu muhimman abubuwa bakwai da ya kamata a sani game da ranar da aka kirkira don tunawa da gudunmawa da sadaukarwar ma'aikata wajen cigaban kasa kamar yadda The Punch ta tattaro.
Abubuwa 7 masu muhimmanci game da ranar ma'aikata ta duniya
1. Ranar hutu ce kasashe da dama. Tarihin ranar kwadago ya fara ne a shekarar 1886 lokacin da kungiyar kwadago ta Amurka ta shiga yajin aiki don bukatar kada ma'aikata su haura awa takwas suna aiki a rana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Ranar kwadago ta samo asali tun a karni na 19 lokacin da ma'aikata a fadin duniya suka fara nuna bukatar a inganta yanayin aiki, karin albashi, da rage awannin aiki.
3. Ana bikin ranar kwadago a sama da kasashe 80, da suka hada da India, Cuba, da China.
Mutane daga sassa daban daban na duniya suna gudanar da tattaki don tabbatar da kare hakkin ma'aikata da kuma kare su daga cin mutunci.
4. Al'adar ranar kwadago da kwanan wata a karni na 19 a Amurka. Ranar 1 ga watan Mayu, 1886 a garin Chicago ma'aikata sun gudanar da yajin aiki don bukatar yin aiki iya awa takwas a rana. Sai dai, daga baya ma'aikata a fadin Amurka sun hade kai tare da yakar yancinsu don samun kyakkyawan yanayin aiki biyo bayan fashewar bam a taron gangamin yan kwadago a sansanin kasuwar Hallymarket.
5. A 1889, gamayyar kungiyoyin jin kai suka hadu a birnin Paris tare da yanke shawarar sanya 1 ga watan Mayu a matsayin bikin ranar ma'aikata.
6. An gudanar da bikin ranar kwadago na farko a India ranar 1 ga watan Mayu, 1923, a Chennai. Labour Kisan Party of Hisdustan ce ta fara shirya bikin ranar farko a watan Mayu. Shugaban kungiyar, Kwamared Singarevelar ya shirya taro har kashi biyu don bikin ranar.
7. Ana bikin ranar kwadago a fadin duniya don wayar da kai kan hakkokin ma'aikata. Yana kuma matsayin tuni kan irin rawar da ma'aikata ke takawa a cikin al'umma.
Shin Babban Bankin Najeriya Tana Shirin Janye Sabbin Kudi, Gaskiya Ya Bayyana
A wani rahoton, Babban Bankin Kasa, CBN, ya yi watsi da rahotanni da ke yaduwa na cewa yana duba yiwuwar janye sabbin takardun naira na N1000, N500 da N200.
Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, CBN ya musunta wannan jita-jitar ne a wata sanarwa da ta fito daga bakin Dakta Isa Abdulmumin, mukadashin direktan watsa labarai na bankin.
Asali: Legit.ng