Shiri Ya Lalace: An Yi Awon Gaba Da Wasu Malaman Addini Cikin Tsakar Dare
- Wasu limaman ɗariƙar katolika sun ga ta kan su bayan an ƙwamushe su a jihar Delta, da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya
- Limaman ɗariƙar suna kan hanyar su ta dawowa daga wata ziyara lokacin da miyagu suka yi awon gaba da su
- Tuni aka yi kira da a sanya fastocin cikin addu'a domin su samu su ƙubuta daga hannun miyagun da suka sace su
Warri, Jihar Delta - Ƴan bindiga sun sace wasu limaman ɗariƙar katolika, masu suna Chochos Kunav da Raphael Ogigba a yankin Agbaro-Otor area, kusa da Warri, babban birnin jihar Delta.
Jaridar Vanguard tace an sace su akan titin hanyar Agbaro-Otor, a daren ranar Asabar lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa Ughelli ko Warri.
Wata sanarwa da wani babban limamin ɗariƙar, Okereke Kizito, ya fitar, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka sacen, Chochos Kunav, yana aiki ne a birnin Ibadan sannan ya kawo ziyara ne ga abokin aikin sa na cocin katolika ta Warri.
Daga nan suka tafi tare domin ziyarar wani faston a yankin Agbaro-Otoe, inda suna kan hanyar su ta dawowa ne aka aka yi awon gaba da su.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanarwar ta yi roƙon a sanya fastocin cikin addu'a domin a samu su dawo cikin ƙoshin lafiya.
Sanarwar tace:
"Muna barar tarin addu'o'i domin a sako su da gaggawa cikin aminci. Mu na addu'ar a duk inda suka tsinci kan su, su kasance cikin samun taimakon ubangiji."
Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa a a ranar Lahadi, inda tace tuni har ta fara bibiyar miyagun da suka sace malaman addinin, cewar rahoton Channels tv.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Bright Edafe, ya tabbatar da cewa suna bakin ƙoƙarin su domin ganin fastocin sun tsira daga hannun ƴan bindigan.
Da Dumi-Dumi: Jiragen Yakin Rundunar Soji Sun Yi Taho Mu Gama a Sararin Samaniya, Rayuka Sun Salwanta
Shekau, Anini, Oyenusi Da Wasu Yan Ta'adda 2 Da Suka Addabi Najeriya
A wani rahoton na daban kuma, mun kawo mu ku jerin wasu ƴan ta'adda da aka taɓa yi waɗanda suka addabi ƙasar nan.
Abubakar Shekau na ƙungiyar Boko Haram yana daga sahun gaba a cikin jerin miyagun da suka addabi ƙasar nan.
Asali: Legit.ng