Hukumar Jarrabawa Ta JAMB Za Ta Saki Sakamakon UTME a Ranar Talata
- Hukumar shiya jarrabawa ta JAMB ta bayyana lokacin da za ta saki sakamakon jarrabawar da aka rubuta a makon jiya
- Hukumar ta kuma bayyana lokacin da za a ba wasu damar sake rubuta jarrabawar a cikin watan Mayu
- Dalibai da yawa na jiran sakamakon jarrabawar JAMB da aka rubuta a makon da ya gabata, ana dar-dar
FCT, Abuja - Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’a ta JAMB ta bayyana cewa, za ta saki sakamakon jarrabawar da aka rubuta a makon jiya na UTME a gobe Talata 2 ga watan Mayu.
Wannan na fitowa ne bayan da hukumar ta zauna zaman taro n gaggawa da masu gudanarwarta a karshen mako a Abuja, rahoton jaridar Leadership.
An yada bayanan da aka tattauna a taron ga manema labarai a ranar Litinin 1 Mayu, 2023 ta hannun kakakinta, Dr. Fabian Benjamin.
JAMB ta bayyana cewa, an samu jinkirin sake sakamakon jarrabawar ne saboda tabbatar da an tantance komai don gudun matsalar da ka iya biyo baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sakamakon taron:
“Hukumar za ta sai sakamakon jarrabawar dukkan wadanda suka yi ta jarrabawar a ranar Talata 2 ga watan Mayu, 2023.”
Wadanda basu rubuta JAMB za su samu damar sake rubutawa
Hakazalika, an yi bayanin abin da zai faru ga wadanda basu samu damar rubuta jarrabawar ba saboda wasu matsalolin da suka auku.
A cewar sakon:
“Yayin da wadanda suka rubuta jarrabawa ke duba sakamakonsu a ranar Talata 2 ga watan Mayum 2023, wadanda rubuta ba jarrabawar amma suka samo tsaiko basu sani ba, za ba za su ga sakamakon ba a madadin haka za su ga sakon sake shirya lokacin da za su sake rubuta jarrabawar.”
Bugu da kari, hukumar jarrabawar ta ce rukuni uku da suka rasa damar rubuta jarrabawar za su sake rubutawa a wasu lokuta.
A cewar JAMB:
“Dukkan daliban da basu rubuta jarrabawar 2023 ta UTME ba a lokacin da aka basu kuma ba laifinsu bane, za a sake tsara jarrabawar a ranar Asabar, 6 ga watan Mayun 2023.”
Ya zuwa yanzu, dalibai a kasar na ci gaba da neman guraben shiga jami'a, amma ana kai ruwa rana da malaman jami'o'in kasar.
Asali: Legit.ng