“A Yanayi Na Yaki Aka Daidaita”: Gwamnatin Buhari Ta Fadi Dalilin Kashe $1.2m Don Kwaso ’Yan Kasar Daga Sudan
- Rahoton da ke bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta kashe $1.2m wajen yin motoci bas don kwashe ‘yan kasarta akalla 2,400 daga Sudan ya jawo cece-kuce
- Biyo bayan wannan lamari, gwamnatin ta fito ta yi bayanin cewa, ta daidaita kan kudin ne duba da yanayin yaki da ake ciki
- Kakakin ma’aikatar jin kai, Rhoda Iliya ta gargadi ‘yan Najeriya da su daina yada bayanai marasa tushe da ke yawo a kafafen sada zumunta
Gwamnatin tarayya ta yi martani game da cece-kucen da ake na cewa ta kashe kudade masu yawa; $1.2m (552,664,441.20) wajen kwaso ‘yan Najeriya da ke Sudan.
Da take martani ga sukar da ‘yan kasar ke yi game da kashe kudin, gwamnati ta yi bayanin dalilin da yasa kudaden suka wuce kima, The Guardian ta ruwaito.
Martanin gwamnati na fitowa ne daga bakin kakakin hukumar jin kai, Rhoda Iliya, jami’an hukumar harkokin waje da na hukumar jin kan; Ambasada Janet Olisa da Dr Sani Gwarzo a ranar Asabar 29 ga watan Afrilu.
A cewar sanarwar:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Cece-kucen da ake na yarjejeniyar kudi $1.2m na hayar bas don yin aiki, bai dace ba sam.
“An daidaita kan farashin ne a yanayi na yaki da kuma yadda ake yawan bukatuwa ga aikin wadannan bas daga sauran kasashen da ke kokarin kwashe ‘ya’yansu.”
Gwamnatin Najeriya ta yaba wa kasashen da suka karbi ‘ya’yanta
Gwamnatin Najeriya ta nemi jama’a da su daina yada wa ko yarda da jita-jitan da ake yadawa a kafafen sada zumunta game da ‘yan Najeriya a Sudan, wasu labaran na karya ne.
Ta kuma kara da cewa, tana aiki tukuru don tabbatar da an kwaso ‘yan Najeriyan da suka makale a kasar ta Sudan da ke fama da yaki, rahoton Vanguard.
A gefe guda, gwamnatin Najeriya ta mika sakon godiya ga kasashen da suka taimaka wajen karbar ‘yan Najeriya hannu bibbiyu a yanayin da suka shiga na matsi a Sudan.
Gwamnati ta tura sojoji su kwaso ‘yan Najeriyan da suka makale a Sudan
A wani labarin, gwamnatin Najeriya ta bayyana tura jirgin sojin sama don kwaso ‘yan Najeriyan da suka makale a yakin Sudan.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da wa’adin tsagaita wuta ya kare tsakanin gwamnatin Sudan da ‘yan tawayen kasar.
Ya zuwa yanzu, tuni ‘yan Najeriya sun fara fita daga kasar, inda ake aikin kwaso su zuwa Najeriya cikin koshin lafiya.
Asali: Legit.ng