Tashin Hankali Yayin da Aka Yi Wa Wasu Matasa Biyu Yankan Rago a Jihar Filato
- Rahoton da muke samu daga jihar Filato na bayyana cewa, an hallaka wasu matasa biyu da ake zargin an yi hakan ne a cikin wata gona
- A cewar kungoyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), an yiwa matasan yankan rago ne basu ba basu gani ba
- Ya zuwa yanzu, rundunar ‘yan sanda bata bayyana wata sanarwa a hukumance game da aukuwar lamarin mai tada hankali ba
Jihar Filato - Wasu tsageru da ba a san ko wasu waye ba sun hallaka wasu matasa biyu a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.
A cewar rahoton da muka samo daga jaridar Aminiya, tsagerun sun yiwa matasa biyu ne yankan rago.
A cewar shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na karamar hukumar, Ya’u Idris, an yiwa matasan kisan gilla ne a wata gona a yau Lahadi 30 Afirilu, 2023.
Meye aka sani game da wadanda aka kashe?
Rahoton da muka samo dai ya zuwa yanzu bai bayyana sunaye da bayanan wadanda aka hallaka ba, duk da kungiyar MACBAN ta fadi yadda harin ya auku.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hakazalika, wakilin Legit Hausa ya kira lambar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Alfred Alabo don jin ta bakinsa, amma bai amsa wayar ba.
Jihar Filato na daya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ke yawan fama da hare-haren ‘yan ta’adda da kashe-kashe marasa ma’ana na tsawon lokaci.
An sha samun lokutan da tsagerun ‘yan ta’adda ke farmakar matafiya da ‘yan kasuwa da ke wucewa da garuruwan da ke jihar, inda ake zubar da jinanen wadanda basu ji ba basu gani ba.
Allah ya yiwa basarake mafi dadewa a kan karaga rasuwa
A wani labarin, kunji yadda aka bayyana mutuwar wani basaraken da ya fi kowanne basarake dadewa a kan karagar mulki a masarautun Najeriya gaba dayansu.
Sarkin, an kuma ruwaito shine mahaifin daya daga cikin ministocin Buhari, kuma ya kasance daya daga cikin masu fada a ji a jihar Cross River da ma Najeriya baki daya.
Ya zuwa yanzu, ahalin basaraken sun shiga jimami, sun kuma bayyana cewa, nan ba da jimawa ba za su fitar da bayani game da yadda jana’izarsa za ta kasance.
Asali: Legit.ng