Gwamna Emmanuel Ya Nada Sabbin Dagattai 149 a Jihar Akwa Ibom

Gwamna Emmanuel Ya Nada Sabbin Dagattai 149 a Jihar Akwa Ibom

  • Gwamnan jihar Akwa Ibom ya amince da naɗin mutane akalla 149 a matsayin Dagacin kauyuka a faɗin jihar
  • Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin naɗin sarauta, Mista Archibong, ya miƙa musu takardun shaidar naɗi
  • Ya ce gwamna ya yi haka ne domin cika alkawarin da ya ɗaukar musu don tabbatar da zaman lafiya

Akwa Ibom - Gwamna Udom Emmanule na jihar Akwa Ibom ya amince da naɗin sabbin Sarakunan gargajiya masu rawanin Dagattai akalla 149 a faɗin jihar.

Leadership ta rahoto cewa gwamnan ya naɗa sabbin Dagattan ne da nufin su yi aiki da gwamnati mai zuwa ta Fasto Umo Ono domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a yankunansu.

Udom Emmanuel.
Gwamna Emmanuel Ya Nada Sabbin Dagattai 149 a Jihar Akwa Ibom Hoto: Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel Hoto: Udon Emmanuel
Asali: UGC

Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin naɗe-naɗen sarauta, Mista Frank Archibong, ya miƙa takardun shaidar naɗa Sarakunan ga majalisar Sarakunan jihar a madadin gwamna.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wainna Ilaihir Rajiun: Wata Dalibar Jami'a Ta Fadi Ta Rasu Tana Kammala Jarabawa

Ya miƙa baki ɗaya Satifiket ɗin shaidar naɗin ga majalisar sarakunan Akwa Ibom domin rabawa mutane 149 da gwamna ya amince a naɗa su Dagacin ƙauyukansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake miƙa shaidar naɗin, kwamishinan ya taya su murna bisa wannan sabon matsayi da Allah ya basu kana ya yaba musu bisa hakuri da juriyar da suka nuna.

Ya ƙara da cewa gwamna ya yi wannan naɗin ne domin cika alkawarin da ya ɗaukar musu.

Ya kuma gode wa Sarakuna iyaye bisa haɗin kan da suka baiwa wannan gwamnatin, inda ya ce gwamnati mai ci ta ba da fifiko kan walwala da jin daɗin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiya.

Kwamishinan ya roki sauran waɗanda har yanzun ba'a basu shaidar naɗi ba da su kara hakuri yayin da gwamnati ke shirin fitar da sabon rukunin takardun shaida nan ba da jima wa ba.

Kara karanta wannan

Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa

Shugaban majalisar sarakuna ta jihar Akwa Ibom, Ntenyin Solomon Etuk, ya gode wa gwamna bisa cika alƙawarin da ya ɗauka na baiwa kowane Dagaci shaidar naɗinsa.

Shugaba Buhari Ya Sake Daga Kidayar Mutane da Gidaje a Najeriya

A wani labarin kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya sake ɗage kidayar yan Najeriya da aka shirya gudanarwa a 2023

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, Buhari ya yaba wa NPC bisa matakan da ta ɗauki na shirya sahihiyar kidaya.

Buhari ya ɗauki wannan matakin ne bayan sauraron inda aka kwana daga shugaban NPC da tawagarsa a fadar shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262