An Yi Ƙarar Wani Tsoho Ɗan Shekara 100 A Kotu Kan Ƙwace Fili Ta N50m

An Yi Ƙarar Wani Tsoho Ɗan Shekara 100 A Kotu Kan Ƙwace Fili Ta N50m

  • An yi karar wani mutum dan shekara 100 da wani dan shekara 61 a kotu kan zargin kwace fili
  • Yan sanda sun gurfanar da Oladepo Ogunlade da Musiliyu Ogundiran ne a kotun Majistare da ke Iyaganku, Ibadan a ranar Juma'a
  • Sai dai wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin suka kuma nemi a bada su a hannun beli, kotu ta amince tare da saka ranar fara shari'a

Oyo, Ibadan - An gurfanar da wani mutum dan shekara 100, Oladepo Ogunlade, da Musiliyu Ogundiran, dan shekara 61, a ranar Juma'a a kotun Majistare ta Iyaganku a Ibadan kan zargin kwace fili da lalata itatuwa na tattalin arziki.

An gurfanar da Ogunlade da Ogundiran ne a kotun kan zargin hadin baki, kwace fili, lalata kayayyaki, yin barazanar tada rikici da aikata abin da ka iya tada zaune tsaye, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun tarayya ta yanke hukunci kan karar da Binani ta shigar game da zaben Adamawa

Gudumar kotu
Ana tuhumar dan shekara 100 da kwace fili ta N50m a Ibadan. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauya mai shigar da kara, Mista Philip Amusan, ya fada wa kotu cewa mutanen biyu sun aikata laifin ne a shekarar 2021 a kauyen Lawani da ke Ibadan.

Amusan ya yi zargin cewa wadanda aka yi karar da wasu da ake nema, sun kwace eka 25 na fili da kudinsa ya kai Naira miliyan 50, mallakar wani Mista Wasiu Lawani.

Ya yi zargin cewa kuma sun lalata wasu itatuwa masu daraja na tattalin arziki kamar itacen kwakwa, kwakwan manja, cocoa da kudinsu ya kai N800,000 yayin da suke barazanar tada rikici.

Amusan ya ce wadanda aka yi karar sun aikata abubuwan da ka iya tada rikici ta hanyar lalata itatuwan da babban motar rusau wato bulldoza ba tare da dalili ba.

Laifin, a cewar dan sandan, ya saba tanade-tanaden sashi na 516, 451 da 249 (d) na dokokin masu laifi na jihar Oyo ta 2000.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: An Kori Mataimakin Shugaban APC Da Wasu 7

ya kara da cewa abin da suka aikata sun ci karo da sashi na 6, 4, da 7 (1) na dokokin kare kadarori na jihar Oyo, 2016.

Wadanda aka yi karar sun musunta a gaban kotu

Sai dai wadanda aka yi karar sun musanta aikata laifin da ake tuhumarsu.

Alkaliyar kotun, Misis O.A. Akande, ya bada belin wadanda aka yi karar kan Naira miliyan 5 kowannensu tare da mutane biyu da suka tsaya musu.

Ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 14 ga watan Yuni kamar yadda NAN ta rahoto.

An Yi Karar Magidanci A Kotu Saboda Auren Mata 5, Alkali Ya Yanke Hukunci

A wani rahoton daban kun ji cewa wan gurfanar da wani Awaisu Jibril a gaban kotun musulunci da ke zamanta a Rigasa Kaduna kan zarginsa da auren mata biyar.

Sufeta Samba Maigari, mai gabatar da kara ya fada wa kotu cewa wani Musa Abdullahi ne ya kai korafi caji ofis na Rigasa kan batun, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Assha: Kakakin majalisa ya tafka wawura, EFCC ta gurfanar dashi da wasu 2 a gaban kotu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164