An Kame Wani Matashin da Ya Kwace Wayar Wata Mata a Kano, Ya Bi Ta da Gudu Zai Soka Mata Wuka
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kame wasu ‘yan daban da suke addabar mutane da yawa a jihar da ke Arew maso Yammacin Najeriya
- An kama matashin da ya nemi sokawa wata makta wuka bayan da ya kwace wayarta, lamarin da ya tunzura wasu ‘yan daba
- Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike kafin daga bisani rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da matashin da sauran tsagerun
Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kame wani matashi mai suna Ibrahim Muhammad bisa kama shi dumu-dumi da laifin yiwa wata mata fashin waya tare da yunkurin soka mata wuka.
A wani bidiyon da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya yada, matashin ya amsa laifinsa tare da bayyana yadda ya aikata barnar.
A cewar matashin lokacin da yake ba da labarin abin da ya faru, ya bi matar ne tare da kwace wayar da ke hannunta bayan yi mata barazana da wuka.
Daga baya, ya bi ta domin ya soka mata wuka, lamarin da ya tsorata ta kafin daga bisani ‘yan kwamiti a yankin da lamarin ya faru su kama shi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mata ta jefar da jaririnta mai watanni
A cewarsa, bai san matar na dauke da jariri a bayanta ba, don haka da ya yi kokarin bin ta sai ta kwance yaron ta fece a guje.
Wasu ‘yan daban da aka kama a gefe guda a irin wadannan laifukan sun nemi a basu shi su hukunta shi daidai abin da ya aikata.
Sun ba da labarin yadda matashin ya yi yunkurin cutar da ita matar, inda suka ce sam bashi da imani da tausayi.
A halin da ake ciki a yankin Arewacin Najeriya, sace waya da raunata mutane ya zama ruwan dare daga ‘yan daban da ke addabar mazauna.
An yankewa matashin da ya watsawa budurwarsa ‘acid’ hukunci
A jihar Legas, an yankewa wani matashi hukuncin zaman gidan yari na shekaru bakwai bisa aikata laifin watsawa budurwarsa ruwan acid mai kone jiki.
Rahoton da muka samo ya bayyana yadda matashin ya samu budurwar tasa da wani a otal, inda ya watsa musu acid ta taga.
Rikicin soyayya na sanya matasa a duniya aikata ayyukan dana-sani, musamman yadda ganin yadda ya faru da wannan matashin.
Asali: Legit.ng